Siyasa

[Siyasar Kano] Hidaya Ahmad ta Dagawa Hon. Fa’izu Alfindiki Yatsa Kan Taba Mutuncin Maimartaba Sarkin Kano

[Siyasar Kano] Hidaya Ahmad ta Dagawa Hon. Fa’izu Alfindiki Yatsa Kan Taba Mutuncin Maimartaba Sarkin Kano

 

Maimartaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi || ya ja hankalin al’ummar jihar Kano kan su zauna lafiya biyo bayan rashin kammaluwar zaben gwamnan jihar da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC tayi.

 

Tun kafin zaben dai Sarkin Kano ya sha kiran al’ummar jihar kan su kaucewa siyasar sara suka da cin mutuncin juna, musamman a yayin addu’ar Zaman lafiya da Maimartaba Sarkin ke jagoranta kowane mako a babban masallacin jumu’a na garin Kanon.

 

Sai dai a wani salo da za’a iya cewa mai neman kuka ne aka jefeshi da kashin awaki, kiran Zaman Lafiya da Maimartaba Sarki keyi bai yiwa wani sashin siyasa na jihar dadi ba, inda aka hangi wani mataimaki na musamman a Gwamnatin jihar mai ci wato Hon. Fa’izu Alfindiki ya wallafa kalaman batanci ga mai martaba sarkin a shafinsa, hausawa sukace waka dai a bakin mai ita tafi dadi, duba wani daga cikin post din da yayi: –

Ba wannan ne dai karo na farko da Hon. Alfindiki ya saba yin irin wannan katobara ba, duba wasu a hotunan dake kasa: –

A kwanakin baya ma dai an samu wani dan siyasa Hon. Abdulmajid Dan Bilki Commander wanda yayi kalaman batanci ga maimartaba Sarkin wanda hakan ya sanya tashar Freedom Radio Kano ta dakatar dashi daga shiga tashar domin kare muhibbar mai martaba sarkin.

 

Sai dai a wani salo na bajinta wata matashiyar ‘Yar Jarida daga jihar Kano mai suna Hidaya Ahmad wadda kuma itace shugabar Gidauniyar Tallafawa Mata Masu Fama da Cutar Yoyon Fitsari ta Hidaya VVF Aid Foundation  ta wallafa kakkausan bayanan Martani na nan take zuwa ga wannan dan siyasa, kamar yadda kuke gani a kasa:-

Al’ummar jihar Kano da dama sunyi alla wadai, da wannan danyen aiki da wadannan ‘yan siyasar ke aikatawa a shafukan sada zumunta.

 

Allah ya kyauta.

 

Basheer Sharfadi

17-03-2019.

 

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *