Ra'ayoyi

Ko Ka San Me Ya Haifar Da Matsalar Kidnappers? -Mahmud Galadanchi

DOLE A SAMU KIDNAPPERS A CIKIN MU.

Mahmud Labaran Galadanci
Mahmudgaladanci@gmail.com
09061767254

Gwamnatocin mu na kowane mataki tun daga tarayya har zuwa local governments basu shiryi magance matsalolin garkuwa (kidnapping) da ake yi da mutane ba, ko hanyar magance matsalar basu yi ba. A nawa hangen kuma wanna matsala ce mai saukin magancewa sai dai an bar kari tun ranar tubani, an bar maganin a baya a dalilin sakaci da rashin sanin matsalar da hakan zai haifar a nan gaba. Yankin arewacin kasar nan bamu san wannan matsalar ba sai a ‘yan shekarun nan gashi yanzu abun yana ta tsamari.

Na saurari wata ‘yar gajeriayar waya da ta faru tsakanin yan matan da aka yi garkuwa da su ‘yan Zamfara state, abun tausayi abun jimami da bakin ciki. Duk wanda ya saurari wannan waya da yaran suka yi da dan uwan su sai yaji kwalla a idon sa saboda tausayawa amma har yanzu ban ji wani yunkuri da gwamnatin jihar Zamfara ko tarayya tayi ba akan kubutar sa rayuwar wadannan ‘yan mata ba. Abun nan yana batawa duk wani mai rajin kare hakkin dan Adam rai ko shakka babu.

Matsaloli ne da yawa suka hadu suka samar da ta’addancin garkuwa da mutane amma babba a cikin su shine tashin aikin yi. Masu wannan aika-aika matasa ne wadanda ko dai sun yi karatu ko basu yi ba. Shi saurayi/matashi idan ya zama yana zaune baya wani aiki yana zama barazana ne ga zaman lafiyar al’ummar da yake cikin ta. Idan hukuma bata bashi aikin yi ba shi zai nemawa kan sa aikin ko da kuwa maras kyau ne. Idan ya buga ya rasa kyakkyawan aiki ko da mummunan ne yazo karba zai yi kuma yayi don yana neman hanyar da zai yi rayuwa ne ko ta halin yaya.

A wani bangaren rashin aikin yi ya taka rawa muhimmiya wajen samar da kidnappers a kasar nan. Bari mu dauki bangare daya na matasan da suka yi karatu na degree da HND wadanda suke da damar bautawa kasa (NYSC). Tun daga shekarar 2015 alkaluman masu bautar kasa karuwa yake da sama 40% duk shekara. A shakarar 2015 an yiwa sama mutane 220,000 rigista ta bautar kasa. A shekarar 2016 mutane sama da 260,000 ne suka yi rigista sanna a shekarar 2017 kusan mutane 300,000 ne suka yi rigista don fara bautar kasa. Kullum abun gaba yake don wannan shekarar kuma sama da mutane 350,000 ne suka yi rigista don fara bautar kasa. Idan ka hada lissafin zaka ga sama da graduates 870,000 ne suka yi bautar kasa a tsakanin shekara uku kawai. Tun daga shekarar 2015 kuma ba’a samarwa da wadannan graduates aiki ba. Masu aiki a cikin ba zasu fi 200,000 wanda a hakan ma ba lallai su kai. Ta yaya wadancan ragowar marasa aikin ba zasu samarwa da kan su hanyar rayuwa ba? Gwamnati tana da muhimmiyar rawa wajen ci gaban wannan matsala ta garkuwa da mutane.

Wannan a wani bangaren kenan, ban tabo bangaren wadanda su kuma basu yi karatun ba don sun fi graduatea din yawa. Sannan ban tabo wadanda suka yi diploma, NCE da ire-iren bangarorin da basu yin bautar kasar. Ta kowane bangare ka kalli abun zaka ga cewa matsalar garkuwa da mutane tana da alaka da rashin aikin yi.

Ta hanya guda za’a magance wannan matsalar shine samarwa da matasa aikin yi don don shagaltar da su aikin da ya kamace su ba ta’addanci ba.

Ina rokon Allah ya kubutar da ‘yan biyun nan ya kawo mana karshen wannan matsaloli a kasar nan gaba daya.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *