Uncategorized

NAZARI AKAN KISAN DA AKE YIWA ‘YAN SHI’A A NIGERIA.

Mahmud Labaran Galadanci
Mahmudgaladanci@gmail.com
09061767254.

Al’amarin kisan ‘yan shi’a a kasar nan yana bukatar nazari da kyakkyawan hangen nesa mai zurfi don gane bakin zaren da kuma kokarin kwatanta adalci. Kisan rayuka a kasar nan musamman a wannan shekarar da muke ciki ya ta’azzara ya zama ruwan dare ya shiga ko ina. Abu ne mai wahala a wayi gari a tashi baka samu rahoton rashin rai daga wani bangare na wannan kasa ba. Kowane mutum akwai yadda yake kallon kisan da ake yiwa ‘yan shi’a tun bayan faruwar al’amarin da yayi sanadiyar kama shugaban Shi’a na Nigeria, malam Ibrahim Zakzaky. Kowane mutum akwai ta fuskar da yake kallon al’amuran amma zan yi nazarin kowacce fuska wajen fito da abun fili don mai neman gaskiya da kyakkyawar zuciya ya fuskanta.

Daga cikin musulmi akwai masu goyon bayan kisan da ake yiwa ‘yan shi’a wanda bayan faruwar kashe dubban mutane a Zari’a an samu wasu daga cikin malaman addinin da suka fito suka nuna goyon bayan su dari bisa dari da wannan kisa da aka yi. Sai dai bana tare da wadannan mutane masu jin dadi don na yiwa abun kallo na tsanaki da adalci. Addinin musulunci bai koyar da gaba da kiyayya a sakamakon sabanin fahimta ba, hasali ma ya bawa kowane dan Adam damar ya zama cikin masu imani ko ya kafirce. Rayuwar manzon Allah ta ishe mu misali don ya zauna da kafirai a Madina har bayan wafatin sa kuma ba’a samu cewa ya taba yin murna da wani abu na bakin ciki da ya same su ba ko kadan. A irin kyakkyawar halayyar manzon Allah wadda Allah SWT ya bamu labari a cikin littafin sa ba zai yiwu ya kasance mai wannan mummunan hali ba. A takaice, ga dukkan wanda ya fuskanci addinin nan da kykkyawar fahimta zai gane cewa Allah SWT ya wajabta mana kaunar juna da tausayawa juna ko da ace ga wanda ba musulmi ba ballantana wanda yake amsa sunan musulmi. A irin yadda addinin musulunnci ya koyar da jin kai da tausayi ko dabbba ma abar a tausaya mata ce ballantana mutumin da Allah yace ya girmama shi sama da komai sannan ya girmama jinin dan Adam. Idan muka kalli abun ta wannan fuskar zamu gane cewa zazzafar akida ce take rufewa mabiya da malaman da suke bayyana jin dadin su ga kisan da gwamnati tayi kuma take yiwa yan shi’a a kasar nan.

Mutane da yawa suna dogara da wasu dalilai marasa karfi ko na sisin kwabo wajen kare goyon bayan su ta’addancin da aka yiwa mabiya shi’a a kasar nan. Abunda ya faru tsakanin shugaban Sojojin kasar nan da ‘yan shi’an a shekara ta 2016 yana daga cikin dalilan da suke dogara da su amma a kwanakinnan abunda yake na zahiri ya karyata wannan al’amari dari bisa dari don kuwa a kwanakinnan aka samu wata kabila a garin Jos suka kashe babban jami’in soja amma ba’a kashe su kamar yadda aka kashe yan shi’a a Zari’a ba. Hankalin ka zai auna maka wannan al’amura guda biyu, wadannan Christians kashe soja suka yi gaba da ya suka rasar masa da rayuwar sa amma su kuma ‘yan shi’a tarewa soja hanya kawai suka yi! A hankalce wannne ne yafi laifi? Amma aka kashe wadanda suka tarewa soja hanya kuma ba ‘a nan ta tsaya ba har gidajen su aka bisu aka rika kashe su ana kona musu gidaje. Shi yasa nace lamarin yana bukatar duba na tsanaki da adalci.

Mu dawo kan abunda ya faru a satin nan a garin Abuja tsakanin jami’an tsaro da ‘yan shia din a dalilin zagayen “Arba’in” da suka saba gabatarwa duk shekara. ‘Yan shi’a sun saba wannan zagaye duk shekara sannan muzaharar mabiya shi’a musamman tun bayan kama malamin su da aka yi ba sabon abu bane a fadin kasar nan. A dalilin zagayen muzaharar tsare malamin su kawai an kashe musu mutane babu adadi a tsakanin wannan shekara biyun. Shi kan sa lamarin tsare Malam Zakzaky yana bukatar duba da idon basira matuka da gaske. A tsarin kasar nan, kotu tana bawa kowanne bangare umarni kuma yayi biyayya akan dole amma jagororin kasar nan sun take umarnin kotu da ta bayar akan a saki Mal zakzaky har ma a bashi diyya a dalilin kotu ta same shi babu laifi kuma ta wanke shi. Amma har yanzu gwamnati tana tsare da shi kuma ta kasa bayyana dalilin ci gaba da tsare shi. Wannan ne ya tabbatar da cewa gwamnati tana da wani boyayyen kuduri akan sa. Idan da ace an bi umarnin kotu an sake shi duk wannan kashe kashen ba zasu biyo baya ba.

A satin nan an samu mummunan arangama tsakanin jami’an tsaro da mabiya shi’a a garin Abuja kamar yadda na fada a baya. Faruwar wannan lamari yana bukatar kallo na nutsuwa sosai. An kashe mabiya shi’a sama da mutane dari hudu haka kawai ba tare da laifin komai ba. Duk wani mai kishin dan Adam zai ji rashin dadi a dalilin faruwar haka don ya saba da dokar kasa. ‘Yan shi’a suna da hurumin fitowa su gudanar da al’amuran su na addini kamar yadda kowanne dan kasa yake da wannan damar amma ana kokarin hana su wannan dama.

Idan muka kalli al’amuran nan muna bukatar mu dakatar da faruwar wadannan kashe kashe da ta’addanci da ake yiwa ‘yan kasa. Yanzu mene maganin wannan lamari? Idan muna son samu maganin wannan al’amura muna bukatar kallon kowanne bangare don bangare daya ba zai kawo maganin abun ba.

  1. Gwamnati: Gwamnati bata da dalilin hana wani dan kasa gudanar da al’amuran sa na addini ko na al’ada kamar yadda kundin tsarin mulki ya bayar da dama. Gwamnati tafi kowane bangare rawar takawa don magance wannan lamari. Ci gaba da tsare Malamin shi’a Malam Zakzaky ba tare da dalili ba sabawa dokar kasa ne don kotu ta wanke shi kuma ta bada umarnin sakin sa. Idan gwamnati zata yi duba da idon basira zata gane cewa tsare malamin nan ne sababin wadannan al’amura. Bayyana rashin adalci ga wani bangare na ‘yan kasa shine abunda yake kawo faruwar ta’addanci. Daga lokacin da wanda ake zalinta yayi bore matsala ce zata faru babba.

  2. Shi’a da Malaman su: su dakatar da dukkan wani muzahara da suke yi don tsare rayukan mabiyan su tunda hakan yana jawo kashe su. Akwai hanyoyi da yawa wadanda zasu iya bi na neman hakkin su duk da an basu hakkin amma gwamnati ta danne. Yana da kyau su gane girman rai yafi komai a addinin musulunci.

  3. Malaman musulunci: Su fito su fadawa gwamnati gaskiyar al’amari na rashin goyon bayan su ga kashe al’umma bada hakkin su ba. Rashin hakan ne yasa har Gwamnatin take ci gaba da kashe mabiya shi’a din. Idan da ace musulmi suna da kwakkwarar murya guda daya wadda zasu yi magana kuma maganar tayi tasiri da ba zaa kawo har wannan lokacin ana samun irin wannan kashe kashe ba.

  4. Jama’ar gari: Suyi fito na fito da wannan zalinci don idan basu yi hakan ba suma watarana abun zai shafe su.

Fata na dai a ko yaushe bai wuce Mu rika Aiki Da hankali ba!

2 COMMENTS

  1. Allah T ya ganar damu yasa mugane sannan muyi amfani da hankalin da Allah T yabamu wurin ganewa da aiki da abunda ya tabbata gaskiya Ameen

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *