Labarai

Kotu Bata Isa Tahana Yajin Aiki Ba – TUC

A yau Juma’a Shugaban kungiyar ‘yan kasuwa ta Trade Union Congress reshen jihar Kwara, Alhaji Kola Olumoh ya bayyana cewa, umarnin kotun masana’antu ba za ya hana kungiyar kwadago dirfafar yajin aiki a kasar nan ba. Alhaji Olumoh ya bayyana hakan ne cikin babban birni na Ilorin yayin ganawarsa da manema labarai dangane da umarnin kotun masana’antu ta zartar na hana kungiyar kwadago shiga yajin aiki da ta kudirta a ranar 6 ga watan Nuwamba. Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ta ruwaito shugaban kungiyar ta TUC ya bayyana cewa, wannan umarni na kotun ga kungiyar kwadago wani tuggu ne na kawo rudani a kasar nan sabanin wanda da take fuskanta a halin yanzu.

Rahotanni sun bayyana cewa, kungiyar kwadago ta shirya shiga yajin aiki a kasar nan sakamakon rashin amincewar gwamnatin tarayya da kuma ta jihohi wajen tabbatar da N30, 000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata a kasar nan.

Olumoh ya kara da cewa, shawarar kungiyar kwadago ta bukatar N30, 000 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata tayi dace da daidai sakamakon yadda ‘yan siyasar kasar nan ke cika lalitarsu da makudan kudi na albashin su.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *