Uncategorized

INA MUKA DOSA!

Aliyu Assufiy Algambiawiy

Algambiawiy@gmail.com

Nigeria kasace ta Allah ya albarkaceta da mutane mabanbanta, banbancin na addini, qabila, ra’ayi, tunani, tsari da makamantansu. Tun bayan samun yanci daga turawan mulkin mallaka, al’ummar wannan kasa suke tarayya wajen cicciba qasar da kokarin sama mata mafita, ba tare da la’akari da banbancin da ke tsakani ba. An fusknaci juna a matsayin mutane guda masu suna daya, wato yan Nigeria, wanda wanzuwar hakan a wancan lokacin ya haifar da nasarorin da muke gani a yau. Saidai a yau mun wayi gari cikin wani irin yanayi na sauyi daga yanda muka faro. mun wayi gari muna kallon banbance banbancen mu na ra’ayi, qabila, addini da kuma tsari a matsayin wata ga6a da zamu nuna kishi ma kawukanmu kadai, abinda ake siffantawa da son kai ko son zuciya ya mamaye tsakaninmu, ta yadda soyayya da taimako ya fara disashewa a mu’amalar yau da kullum.

Wannan sauyi ya janyo cutuwa mai tsanani tsakanin al’ummar qasar nan, kashe kashe a tsakanin mu, nuna halin ko in kula ga zaluntar sashenmu, da sauran abubuwan da muke gani yau suna gurbata al’ummar mu. Ga karamin misali da a yau muke ganin illar sa a tsakankanin al’umma, Yan Qabilar Birom dake jos, wanda tsawon shekaru suke cutar da qabilun da ba nasu ba a yankunan su. Suna da damar rayuwa a cikin qabilun da ba nasu ba, a daidai lokacin da rayuwar waninsu a yankinsu ke cikin hatsari. Yau sun kashe wane gobe sun koma ga wane. Hatta wadanda ke da haqqin kwantar da tarzomar basu tsira ba daga zaluncin wannan qabila ba, a kwanakin nan aka samu rahoton sun kashe wani babban soja.

Wani abu da ya fi haka muni shine daga bangaren ita kanta hukumar da gudunmawarta wajen ciyar da al’ummar mu baya.
Hukumomin kasar nan, musamman na tsaro sun taka muhimmiyar rawar gani wajen ci bayan wannan al’umma, a matsayin ta na hukuma data ginu kan taken “Service and Protection with integrity” sun rasa wannan siffa ta integrity a tattare dasu. Babu ita ga wanda tare masa hanya zata jawo kashe dubban rayuka, hakanan babu ita ga wanda tare masa hanya zata kaishi ga rushe gidaddaji da wuraren ibadar al’umma. Babu ita ga wadanda suke damu maslahar aljihunsu kan tabbatar da gaskiya, hakanan babu ita ga wadanda zasu bada kafa ga wani sashi na mutanen qasa su cutar da sashensu. An rasarwa da qasar nan qimanta jini da rayuwar al’ummarta a tsakanin hukumomin da ke da alhakin hakan, da kuma alummar da ke rayuwa a cikin ta. Dan qabila kaza na kashe dan qabila kaza, haka a tsakanin addinai mabanbanta, haka a tsakanin fahimtu mabanbanta a addini guda, haka a tsakanin ra’ayiyyika mabanbanta a qarqashin fahimtar addini.

Mai neman mafita zai tambayi cewa ina muka dosa? Ina muka nufa a sanda al’ummar mu ke fama da wannan matsalar, Shuwagabannin mu kuma sun shagala da fafutukar kujeru da madafun iko? Wannan na yunqurin ganin kota halin qaqa ya kai ga nasarar samun mukaminsa koda kuwa hakan zata samune takan kashe dubban al’umma, wancan na yunqurin kashe abokin hamayyarsa sabida yana zama masa barazanar komawa ko tabbatar takararsa. A taqaice dai tun daga masu mulkin, hukumomin , da kuma al’ummar basu da wani hadafi na ciyar da al’umma gaba sai abinda yake maslaha ga kawukansu. Ina makomar mu a gobe kenan? Ina muka dosa?

Magantar wannan matsalar aiki ne da ya rataya a wuyan duk wani dan Nigeria, dole sai mun mai da kawukanmu jakadun zaman lafiya, mun rungumi juna tare da kaunar juna ba tare da la’akari da banbancin qabila ko addini ba, sai kun yarda dukkan ku yan uwa ne a yan Adamtaka (Humanity). Wannan shine kadai abinda zai dawo kana da abinda muka rasarwa kanmu tsawon shekaru.

©Algambiawiy
2018

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *