Rahotonni

An tsinci kafar mutum sukutum a jihar kano

A wani abu mai matukar ban tsoro An tsinci kafar bil’adama sukutum a unguwar sabon gari dake  burnin kano.

Al’ummar wannan yanki dai sun wayi gari ne da ganin wannan abun al’ajabi da misalin karfe 07:00am na safiyar wannan rana ta juma’a a wani gini dake bayan katafaren gidan siniman nan ta ELDORODO darke unguwar sabon gari a jihar.

mazauna yankin sun shidawa wakilin mu cewa suna fito aiki ne suka tsinci wannan kafa a yashe kafin daga bisani jami’an yan sanda su kona ta.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *