Rahotonni

Uwar Gidan Babban Hafsan Rundunar Sojin Kasa, Laftanar Janar Buratai Ta Yiwa Al’ummar Jihar Taraba Sha Tara Ta Arziki.

Daga Muhammad Auwal
Uwar gidan babban hafsan rundunar Sojan kasa, Laftanar janar Tukur Yusuf Buratai, Ummu Kulsum Buratai ta kaddamar da wasu rukunin azuzuwa da kuma dakin gwaje gwajen kimiyya na zamani da ta gina ma makarantar sakandare dake garin Mutum Biyu na jahar Taraba.
Ko Da yake dai bata samu damar halartar taron ba, amma ta samu wakilcin Hajiya Rabi Mohammed, uwargidan kwamandan bataliya ta 20 dake garin Serti na jahar ta Taraba, wanda ta bayyana cewa ta dauki nauyin aikin ne sakamakon burinta na ganin ta samar da ingantaccen ilimi. “Na mayar da hankalina ga ayyukan kiwon lafiya da ilimi ne saboda sune ginshikai guda biyu mafi muhimmanci ta wajen samar da cigaba mai daurewa a tsakanin kowanne al’umma. “Ruwa shine rayuwa, lafiya kuma jari ne, ilimi kuma shine babban makamin da mutum zai iya amfani da shi wajen kawo sauyi mai inganci a Duniya.” Inji ta.
Haka zalika Ummu ta yi kira ga matasan yankin da su guji ta’ammali da miyagun kwayoyo da zinace – zinace, inda ta bukace su dasu rungumi zaman lafiya da juna, domin ta haka ne kadai zasu samar da kyakkyawan cigaba mai daurewa.
A nasa jawabin, shugaban karamar hukumar Gassol, Alhaji Yahuza Ya’u ya bayyana godiyarn sa ga uwargidan babban hafsan rundunar sojin kasa, Ummukulsum Buratai, inda yace ya gudanar da ayyuka masu muhimmanci da dama don amfanin matasan yankin. Daga karshe yayi kira ga sauran yayan garin mutum biyu da Allah ya daukakasu da suyi koyi da Hajiya Ummukulsum wajen samar da ayyukan da zasu kyautata rayuwar al’ummar garin gaba daya.
AREWATIMES.COM.NG

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *