BUWAYI GAGARA MISALI

Tarihin Yakin Duniya Na Farko

TARAHIN YAKIN DUNIYA NA FARKO.

SA’ID AMINU SAID @ 08163808484 TES KAWAI

Masu karatu Assalamu Alaikum barkan Mu da wannan lokaci da kuma haduwa ta cikin sabon shafin BUWAYI GAGARA MISALI, shafin da zai fara yin binkice tare kuma da zakulo muku tarihin wadansu muhimman abubuwa da suka wakana a wannan duniya tamu ta BUWAYI GAGARA MISALI domin dai mu al’ummar wannan zamani muyi izina da su wadancan lamura wanda zai fara zuwar muku ta wannan gidan jarida mai Albarka na AREWA TIMES Mabuga labaran gaskiya.

Zamu fara da gabatar da TARIHIN YAKIN DUNIYA NA FARKO.

Daga cikin abubuwan da suka faru a yan’ kwankin nan akwai –

Mutanen Bosnia suna bikin cika shekaru 104 da kisan Archduke Franz Ferdinand, Yariman Austria a birnin Sarajevo a shekara ta 1914, al’amarin da ya yi sanadin haifar da yakin duniya na farko.

A tsakiyar birnin Sarajevo ne wani dan Yugoslavia dan kishin kasa mai suna Gabrilo Princip ya bindige Archduke Franz Ferdinand da Matarsa, lamarin da ya jefa duniya cikin yaki na tsawon shekaru hudu.

Sai dai kuma akwai rabuwar kai tsakanin mutanen Balkans da suka hada da Sabiyawa da Musulmin Bosnia da sauran kabilun yankin game da al’amarin. Wannan ne kuma ya hanawa shugabannin yankin haduwa a waje daya domin gudanar da bikin a yau Assabar.

A kasar Austria ma Jikoki da dangin Franz Ferdinand da aka kashe zasu gudanar da bikin tunawa da kisan shi yau tsawon shekaru 104.

Sabiyawa dai sun dauki Gavrilo Princip a matsayin Jarumi wanda ya kwato masu ‘yanci inda wasu Sojojin Serbia ke bauta masa, amma Musulmin Bosnia suna masa kallon Dan ta’adda.

Yakin an fafata mafi yawansa kasashen Turai, amma ya zama na farko da ya kunshi galibin kasashen duniya, saboda lokacin Turawa suna mulkin mallaka.

Yakin ya barke a shekarar 1914 bayan kisan yarima Archduke Franz Ferdinand na Ostiriya a birnin Sarajevo na Bosniya. Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen Turai na taimakawa ko kare juna daga wata barazana ta taimaka wajen barkewar yakin.

zamu cikin a lokaci na gaba in Allah ya yarda.

SA’ID AMINU SAID @ 08163808484 TES KAWAI

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *