Ra'ayoyi Rahotonni Shirye-Shirye

Me Yasa Masu Mulki Ke Bautar Da Talakawa -Aliyu Sufiy Algambiyawy

MEYASA MASU MULKI SUKE BAUTAR DA TALAKAWA.

Bautarwar masu mulki ga talakawa abune da ya samo asali tsawon lokaci a tarihi, domin duk inda akace ga shugaba na wata al’umma, sai an samu wani nau’i na bauta da talakawa ke masa. Bauta anan bada ma’anar ibada ba, bauta da ma’anar rasar maka da yanci, da kuma tilasta. Idan muka koma tarihin duniya, zamu ga cewa talauci bai taba yankewa a tsakanin al’umma ba, kuma talakawa ababen warewa ne a cikin kowacca al’umma. Talaka mutum ne mai rauni, wanda samunsa baya wadatar dashi cinsa da shansa na yini guda, rayuwarsa kullum cikin fadi tashi ne da jajircewa kan abinda ya dogara dashi na sana’a dan samun mafita.

Mai mulki kuwa mutum ne da ya siffantu da jin izza, taqama da kuma son isa, wanda yake yalwace da dukkan ababen jin dadin rayuwa da zasu wadaceshi su kuma wadaci dubunnan al’ummar dake kewaye dasu. Wannan tasa bayan karfi na mulki, yake da wani iko na musamman akan talaka, saboda ya mallaki abinda duk wahalar da talaka zai sha a rayuwa dan samun tsakure ne na irin abinda ya mallaka. Buqatuwar talaka ga abinda mai mulki yake dashi, na daga manyan Dalilan dake sabbaba Bautar da talaka daga masu mulki. A yadda suke da burin samun izza, da taqama, buqatarka wajensu na samuwa ne kadai idan ka tafi akan shrudansu, wanda a cikine bautar dakai din ke shiga.

Mai mulki na iya tilastar ka dan kana mabuqaci wajensa kayi masa duk abinda yake so ko da baka so, wannan tasa zaka ga a tarihin sarakunan baya, kowannensu yana da wanda yake sashi dariya daga talakawansa, wanda zai masa fifita, wanda zasu ke daukarsa a kafada, wanda zai ke taka gadon bayansa dan ya hau karaga ko abin hawa da makamantansu. Zaka samu ko iyali ne dasu, basa girka musu abinci ko su kawo musu, saidai talakawan da aka sanyawa alhakin hakan suyi. A wasu masarautun ma hatta wanka yiwa sarakunan ake musamman idan ka koma tarihin Athens da Sparta.

A tare da hakan, akwai irin talakawan da suka tsira daga afkawa cikin irin wanann bauta, sune masu ilimi daga cikinsu. Ilimi wata baiwa ce da take daukaka mutum ta kuma bashi wata daraja ta musamman, wannan ne yasa hatta sarakuna da masu mulki su suke neman ma’abota sani saboda nasarar mulkinsu a tsakanin al’umma. Qaramin misali na kurkusa shine Imam Abu Hamid Algazzali, wanda tarihi ya nuna cewa ya taso a faqiri kuma maraya, amma dake Allah ya bashi baiwar ilimi sai da takai Khalifa na wannan zamanin baya sanya mutum a matsayin Amir sai da yardarsa. Ilimi shine kadai abinda mai mulki zai gani tattare da talaka ya muhimmantashi ya kuma kaddarashi. Shiyasa ma’abota hikima suke cewa “Knowledge is power” ma’ana ilimi shine iko.

Sai dai ayau, mun wayi gari duk da irin qima da daraja da ilimi yake dashi, ma’abotansa sa dama basa qaddarashi, domin sun nemeshi ne dan samar wa da kansu wata dama da zasu samu duniya koda kuwa zata kaisu ga wulakanta ilimin. Zaka samu maimakon ace shuwagabanni ne ke bibiyar Malamai dan neman albarkarsu da kuma shawarwarinsu akan abinda ya dangancin mulki da sha’anin al’umma, sai a samu malaman ne ke yawo guraben masu mulkin nan suna rokon alfarmar a gansu, su miqa buqatunsu na gaskiya da na karya, hakan ye jawo shuwagabanni ayau suka maida malamai wadansu mutane da zasu iya amfani dasu dan cimma manufofinsu masu kyau ko marasa kyau, a takaice dai suma masu ilimin na yau basu kubuta daga bautar da kansu ba duk da baiwar ilimi da Allah yayi musu.

Ya ishe mu misali abinda ya faru a jihar kano a ranar 25 ga watan oktoba, 2018 inda bautar da malaman bata tsaya iya ga su ba, saida suka tilasci yara dalibai akan su bar karatunsu na ranar, su fito kan tituna dauke da takardun da basu san menene a jikinsu na, suna yawo a tsakiyar rana kan kwalta da sunan wai marawa gwamnatin baya. Mafi muni kuma Malamansu ke jera su tsaye suna yawo tamkar yan bangar siyasa, sun saida girma da mutuncin ilimin su a dan tumuni kadan, sun kuma dora dalibansu akan jagaliyar siyasa. Yayan talakawa kadai aka iya bautarwa a wannan lokaci saboda kaiwa ga manufar wani mai mulki, a daidai lokacin da akai wasarere da haqqinsu na samun ingataccen karatu.

A takaice dai bautar da talaka da ake yana da alaqa da zuciyar shi talakan ne, domin ko da ilimin, muddin zuciyar bata wadatu da kanta ba, muddin tana hange da kwadayin abinda bata isa mallaka ba, bazata tsira daga wanann bautar ba, mafi girma daga haka kuna kuma rashin sanin kai. Dukkanmu yan adam ne da muke da damar yin rayuwa kamar kowa, kuma Allah ya sanya tausayi da jinkai a tsakaninmu, wannan tasa dole mu tausayawa kanmu a matakin farko, mu san kanmu dan mu tsira daga zaluncin masu mulkarmu.

Marubuci: Aliyu Sufiy Algambiyawy

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *