Ra'ayoyi Rahotonni Shirye-Shirye

Alakar Tsats-tsauran Ra’ayi da Ta’addanci -Mahmud Galadanchi

AKAN TSATTSAURAN RA’AYI DA TA’ADDANCI.

Abu mafi muhimmanci a rayuwar al’umma shine kwanciyar hankali (peace). Rashin kwanciyar hankali ne asalin lalacewar al’umma duk girman ta kuma duk yadda ta kai ga kwarjini. Daga lokacin da aka rasa kwanciyar hankali a cikin al’umma daga sannan ne komai yake fara lalacewa, maimakon a samu ci gaba sai a koma baya. Ci gaban da aka samu a tsawon shekaru goma ana iya rasa su a kwanaki kadan daga sanda aka rasa kwanciyar hankali.
Abun tambayar shine: mene ne abaunda yake jawo tarzoma da rashin kwanciyar hankali a cikin al’umma? Ina kallon wannan amsar ta bangare guda kuma a dunkule wanda duk wani dalili zai iya komawa cikin ta. Amsar nan kuwa itace: abunda yake jawo rashin kwanciyar hankali shine ta’addanci shi kuma ta’addanci(terrorism) yana samuwa ne a dalilin tsattsauran ra’ayi(extremism). Tsattsauran ra’ayi yana iya zama na halayya ne ko kuma a dalilin fahimta ta addini. Tsattsautan ra’ayin da yafi kawo ta’addanci shine na addini. Kaso mafi yawa na mutanen duniya suna rayuwa ne a karkashin dokar addinai mabanbanta wanda a dokar wannan addinin suke gudanar da al’muran rayuwar su na yau da gobe. Suna karbar umarni da hani daga wadannan addinai nasu a kowane lokaci. Babu wani addini a fadin duniya wanda baya koyar da zaman lafiya don sai da zaman lafiya za’a iya gudanar da al’amuran yau da gobe na wannan addinin.
Na karkata akalar dalilin ta’addanci akan “religious Extremism” ne saboda shine a yau duniya take fama da yaki da shi. Mafi yawan ta’addancin da yake faruwa a yau a dalilin addinin ne. Musulmi ya kashe Christian ko Christian ya kashe musulmi, ko wani mai kama da haka. Idan ka kalli abun da idon basira zaka gane cewa dukkan wanda yake amfani da sunan addini yana ta’addanci bai san mene asalin addinin nasa ba. Da ubangaiji yaso da sai ya halicci musulmi a matsayin Christian ko kuma Christian a matsayin musulmi, wani ganin dama ne na ubangiji ya halicce mu masu mabanbantan addinai don mu mu’amalanci juna.
A gefe guda kuma, babban abunda yake jawo “extremism” ko na addini ko a mu’amala shine ganin kowa yana aikata ba daidai ba. Da lokacin da mutum yake ganin kowa batacce ne daga sannan ne yake tsarkake kan sa yake kazanta kowa. Wannan ne matakin da yake girma ya kawo matsalar ta’addanci. ana haifar mutane a garuruwa mabanbanta sai su taso suna ganin al’adar su ko addinin su ne kadai daidai duk wanda baya cikin su batacce ne ko ya halaka, amma sun kasa gane idan da ace a cikin wadanda suke halakarwa aka haife su haka zasu kalli kabilar da suke cikin ta.
A takaice, maganin matsalar tsassauran ra’ayi guda daya ne, yarda da ‘yancin addini, fahimta da kuma ra’ayi. Idan ka yarda kowa zai iya addinin da ya fahimta ba zaka yi masa kallon batacce ba ko kuma wanda ya halaka. Ganin ra’ayin wani a matsayin gurbataccen ra’ayi shima wata matsala ce babba. Daga sanda kake girmama fahimta da ra’ayin wanin ka ba zaka taba jin kaikayi a zuciyar ka ba ballantana ka gudanar da ta’addanci a kan sa ba. Da yawan mutane suna ganin ta’addanci a matsayin kisa ko “attacking ” wanda ba haka bane. Ko magana ce ka fadawa wani wadda ta jawo bacin ran sa ka aikata masa ta’addanci. Bin wannan maganin guda daya shine zai kawo mana karshen tsattsauran ra’ayi da ta’addanci.

Marubuci: Mahmud Labaran Galadanci

3 COMMENTS

  1. Masha Allah
    ya Mahmoud wannan maganace me mahinmanchi sosai,domin kuwa babu abunda yake yuwu wa seda zaman lafiya da kwanciyar hankali,Wanda kuma a halin yanzu sune suke kokarin yimana karanchi,fatan mu a har kullum Allah yabamu zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasarmu ameen.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *