Labarai Siyasa

Takai Ya Kai Kansa Hukumar ‘Yan Sanda A Jiya Litinin

MALAM TAKAI YA AMSA GAYYATAR DA RUNDUNAR YANSANDAN JIHAR KANO TAI MASA.

Dan takarar gwamnan Jihar Kano na Jami’yar PDP, Malam Salihu Sagir Takai ya amsa gayyatar da rundunar yansandan Jihar Kano ta yi masa a yau domin ya amsa wasu tuhuma tuhume da ake masa wanda magoya bayansa suka kashe wani dattijo mai kimanin shekara 70 ta hanyar sara masa gatari akan sa.

Kakakin rundunar yansandan Jihar Kano, SP Majia yace tunda safe Malamin ya kawo kansa zuwa ofishin yansanda, ya bayyana cewa an kai Malam Takai sashin binciken laifuka don ya amsa tambayoyi kan zargin da ake wa magoya bayansa.

Daga karshe SP Majia Yace ya zuwa yanzu sun gano wasu mutane uku da ake zargin suna da hannu a kisan wannan bawan Allah, kuma ana kan cigaba da bincike domin tabbatar da hukunci na adalci akan duk wanda aka kama da laifi.

Rahoto: Ibrahim Rabi’u Kurna

1 COMMENTS

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *