Labarai Ra'ayoyi Rahotonni Siyasa

Meye Gaskiyar Videon Ja’afar Ja’afar??

Meye Gaskiyar Videon Ja’afar Ja’afar??

Tun bayan da jaridar Daily Nigerian mallakar fitaccen dan jarida Ja’afar Ja’afar ta fitar da Videon dake nuna mai girma gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana karbar kudade samfurin daloli wanda ta bayyana a matsayin na rashawa, mutane da dama ke ta cece kuce akai, hakan yasa na gudanar da nawa binciken tare da tuntubar kwararrun masana a bangaren Computer musamman masu daukar hoto/video da kuma gyaransa.

Videon Ja’afar Ja’afar Ya Gamu Da Tasgaro

Videon Ja’afar Ja’afar yazo da tasgaro wanda hakan ya sanya wasu ke da shakku akan videon.

  1. Rashin ganin wanda yake bada kudin
  2. A videon na farko an nuna kwanan wata daban-daban kamar haka 2017-02-10 da kuma 2017-02-12
  3. A video na daya da na biyu mai bayar da kudin an nuna rigarsa iri daya ce
  4. Ba’a nuno tashin gwamna ba
  5. Videon bai dauku yadda ake so
  6. Shin gwamna ya manta da akwai CC Camera a gidan gwamnati ne?

Sai dai duka wadannan ba dalilai ne da zasu rusa cewa ba gwamna Ganduje ne a videon ba, sai dai kawai ace yana da wadannan tasgaron.

A hirar da akayi da Ja’afar Ja’afar a Radio France International (RFI) ya bayyana cewa wani daga ‘yan kwangilar ne ya tsegumta masa irin wannan badakala da gwamnan Kano yakeyi ga ‘yan kwangila kuma a dalilin hakane har ta kai ga yayi amfani da Camera ta Agogo da ta Biro har aka samu daukar wadannan videoyin, sannan videon ba su kenan ba (da sauran kallo).

Idan muka kalli bayanin Ja’afar to rashin bayyanar mai bada kudin ba matsala bane.
Ban-bancin kwanan wata kuma ga wanda ya san computer sai muce kana da video guda biyu amman an daukesu a ranaku daban-daban sai kake son hade su akwai abinda ake kira “joining” to anan zamu iya cewa shine abinda ya faru, ko kuma Ja’afar ne yayi rafkanwar kwanan wata.

Zamowar video da riga daya shima abin tambaya ne a tsawon ban-bancin shekara guda ace da wannan rigar ya sake dawowa, a nan ma ana iya cewa ko dai Ja’afar yayi rafkanwa?

Rashin nuno tashin gwamna da rashin daukuwar video musamman a video na farko wannan ba dalili bane ga duk wanda ya san computer da kuma Video Coverage & Editing domin idan aka hada videon karya sai akayi exporting dinsa a High Quality to za’a ga videon tar-tar wato dai ba Quality din videon ne yake nuna ingancinsa ba.

Me Binciken Mu Ya Tabbatar?

Na bibiya na kuma bincika a karshe dai magana ta gaskiya shine Wannan Videon tabbas mai girma gwamna ne babu kuma wani mahaluki da zai kawo dalilan da zaice ba gwamna bane.

Editing Din Videon Akayi:

Tabbas abinda ake kira da editing shine gyara video amman daukar kan wane a dorawa kan wane abune daban kuma ya saba da abinda ake kira editing domin irin wannan canjin ya sabawa doka.

Ana daukar kai a dora a video amman zaka samu mafi yawa a nan Nigeria abune da akeyi a matsayin Cartoon ko wanda ake bada misali na videon da wasu suka taba hadawa na tsohon shugaban kasa Good Luck da Shekau shima Cartoon ne dole za’a ga ban-banci a jikin su.

Ana Iya Dora Kai A Hoto:

A Nigeria hoto ne ake iya dora kai ya hau ya zauna daram idan ba wanda ya sani ba, ba zai gane ba, misali anyi hakan ga mai martaba sarkin Kano Malam Ja’afar Sheikh Ibrahim Inyass d.s.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kano shima ya bayyana cewa wannan videon kirkirarsa akayi.

Tabbas abin kunya ne ga wanda ya rike mukamin kungiyar ‘yan Jaridu tun daga mataki na jiha har na kasa ace ya rufe idonsa ya fadi haka.

Mataimaki na musamman ga Gwamna akan kafafan yada labarai Hon. Salihu Tanko Yakasai shima yace videon bogi ne.

To muna kalubalantar wadannan mutanen da su kawo dalilan da zasu bayyana hakan.

Mai girma Kwamishinan Raya Karkara Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso yace yana da video sama da Talatin 30 kuma na rashawa kuma idan ya fito dasu za’a ji kunya.

To Don Allah mu masu kishin jihar Kano muna bukatar da shima ya fara sakin nasa kamar yadda Ja’afar ya fara saki.

Ta Yaya Za’a Warware Wannan Batu

Na karanta rubutun Dr. Sa’id Ahmad Dukawa na Jami’ar Bayero, da kuma Bashir Yahuza Malumfashi na Jaridar Aminiya, da kwararren Lauya Barrister Audu Bulama Bukarti kuma naga sun kawo batutuwan da za’a warware wannan batu ga mai bukata sai ya neme su a nan facebook.

Zan dakata a nan amman akwai tacewa a bakina.

Sunana Basheer Sharfadi daga teburin Gaskiya Da Gaskiya Wanda hausawa ke cewa Malam Ya Sayi Malam.
16-10-2018.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *