Addinai Labarai

N500,000 Sun Fito Daga Kudin Masallachin Izala a Kano

N500,000 Sun Fito Daga Kudin Masallachin Izala a Kano

A yau jumu’a 15-10-2018 kotun shari’ar musulunci dake zaune a Rijiyar Lemo dake nan Kano ta cigaba da zaman sauraron shari’a da Malam Ahmad Sabuwar Gandu tsohon shugaban kwamitin masallachin jumu’a na Sheikh Ja’afar Mahmud Adam dake unguwar Sabuwar Gandu ya shigar yana neman shugaban kungiyar Izala ta Jihar Kano Dr. Abdullahi Saleh Pakistan da ya dawo da kudin masallacin har N900,000 da ya ranta.

A zaman na yau Litinin lauyan da ya bayyana kansa a matsayin wanda zai kawo wannan kudi amman bai samu kawowa a makon da ya gabata ba.

A yau lauyan ya kawo kudi har N500, 000 Inda ya bada uzrin cewa sun ajiye kudin ne a “Saving Account” don haka basu da damar cirar kudin baki daya a yau amman sunyi alkawarin kawo cikon kudin a gobe Talata.

A nasa bangaren mai kara Malam Ahmad Sabuwar Gandu ya halarci zaman tare da wasu da ya bayyana a matsayin ‘yan kwamitin dake da ruwa da tsaki akan wannan kudi.

A karshe mai shari’a Ibrahim Bala ya dage wannan kara zuwa gobe Talata.

Allah ya kyauta.

AREWA Times
15-10-2018.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *