Addinai Labarai Rahotonni

N900,000 Daga Kudin Masallachin Izala Sun Kara Yin Layar Zana A Kano

N900,000 Daga Kudin Masallachin Izala Sun Kara Yin Layar Zana A Kano

A ranar Jumu’a 12-10-2018 kotun shari’ar Musulunci dake zamanta a unguwar Rijiyar Lemo a birnin Kano karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Bala ta cigaba da saurarar karar da Malam Ahmad Sabuwar Gandu tsohon shugaban kwamitin masallachin marigayi Sheikh Ja’afar Mahmud Adam Dake Sabuwar Gandu ya shigar yana kalubalantar shugaban kungiyar Izala ta Jihar Kano Dr. Abdullahi Saleh Pakistan akan rashin dawo da cikon kudin masallaci har Naira Dubu Dari Tara N900,000 wanda ya ranta daga kwamitin masallachin.

Asalin wannan batu dai ya samo asali ne tun lokacin da tsohuwar Gwamnatin Kano zamanin Gwamna Malam Ibrahim Shekarau ta baiwa wannan masallaci kudi domin yin gyare-gyare wanda acikinsu ne Shugaban kungiyar ya ranci kudaden da zummar zai dawo dasu daga baya amman hakan bai yiwu ba.

Bayan doguwar shari’a ta shekara da shekaru a zaman kotun na baya da suka gabata wani Lauya ya bayyana da cewa daga kwamitin masallachin Inda yace ya zo da wadannan kudaden kuma kotu ta dage zaman ta kuma sanya wata ranar daban cikin wannan makon don a sake zama domin lauyan ya gabatar da wannan kudade, Amman a zaman kotun da aka sake yi lauyan yazo amman yace bai samu zuwa da kudin ba, hakan ya sanya alkalin kotun ya dage shari’ar zuwa jiya Jumu’a, sai dai a jiya jumu’ar ma lauyan ya gagara sake kawo wadannan kudaden.

Lauyan masu kara ya nemi kotun da ta bada umarnin kamo Shugaban Izalar na jihar Kano.

Sai dai Alkali ya dage shari’ar zuwa ranar Litinin dinnan 15-10-2018.

Allah ya kyauta.

AREWA Times
13-10-2018.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *