Labarai Siyasa

Kisan Kai: ‘Yan Sanda A Kano Sun Gayyaci Malam Salihu Sagir Takai

Kisan Kai: ‘Yan Sanda A Kano Sun Gayyaci Malam Salihu Sagir Takai

Rundunar yansandan Jihar Kano ta bakin kakakinta, SP Magaji Musa Majia ta fitar da sanarwar gayyatar dan takarar gwamnan Jihar a jami’yar PDP zuwa babbar shelikwatar yansanda ta bompai a ranar Litinin 15/10/2018 da misalin karfe 10am na safe.

SP Majia Yace dalilin gayyatar sa domin ya amsa tambayoyi bisa zargin magoya bayansa da sarawa wani bawan Allah mummunan gatari akansa wanda daga bisani ya rasa rayuwar sa.

Ya Kara da cewa magoya bayan Malamin sun kuma cigaba da tafiya suna sare duk wani allon siyasa da bana dan takarar su bane ba.

Lamarin dai ya faru ne a yammacin yau lokacin da Malam Takai ya dawo gida jihar Kano daga birnin tarayya Abuja.

Rahoto: Ibrahim Rabi’u Kurna

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *