Kimiya Labarai

Instagram Ya Kashe Auren Wata Mata a Jihar Kebbi

Shafin Instagram Ya Kashe Auren Wata Mata a Jihar Kebbi.

Auren matar ya mutu ne bayan mijinta ya samu wani ya dora hotonta a shafin sadarwa na Instagram.

Matar da ta nemi na boye sunanta tace wani ne ya yaudareta har ta tura masa hotonta amma daga karshe hakan ya ja aurenta ya mutu.

Matar ta dauki Alkur’ani ta rantse da shi akan cewa wallahi bata mu’amala da maza duk domin mijin ya yadda da ita amma yace ta tafi gidansu kawai.

Tayi kokarin ganin mijinta ya fahimceta amma Yaki saurarta, ta nemi a sata a addu’a akan Allah yasa mijinta ya saurareta ya gane cewa bata yi hakan da gan gan ba kaddara ce kawai ta zo mata.

Matar cikin yanayi na damuwa ta Kasa bayyana yadda akai har ta turawa wani hotonta, amma tace idan har mijinta zai saurareta zata fada masa ko ya akai hakan ta kasance.

Rahoto: Ibrahim Rabi’u Kurna.

1 COMMENTS

  1. Gaskiya tayi kuskuren da bazata Iya gamsar da kowaye ba dalilin da Yasa ta aikawa Wanda ba Muharraminta hotontata ba.
    2-Zamansu zai yi wahala domin zargi ya riga ya shiga tsakaninsa da Ita.
    3-Mafita daya an an itace a nemi manya su shiga maganar domin a “bashi hakuri, sannan ya kwace wayar hannunta, ya canja mata da “Rakani Bandaki” wato yar karama mai tocilan da radio.
    Gani ga wance, ya Isa wance tsoran Allah. Mata ayi hattara. Allah Ya sasantasu, Ya kara rufa mana asiri.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *