Audio DANDALIN NISHADI

In Babu Ke: Matashin Mawaki Khalyperh Damisa Ya Fitar Da Sabuwar Waka

In Babu Ke: Matashin Mawaki Khalyperh Damisa Ya Fitar Da Sabuwar Waka

 

A yau jumu’a 12-10-2018 Fitaccen Matashin mawakin nan Abubakar Adamu Damisa  wanda aka fi sani da Khalyperh Mai wakar LOVER  ya fitar da sabuwar wakarsa mai taken IN BABU KE wakar in babu ke dai ta ja hankalin masoyan mawakin a shafukan sadarwa na yanar gizo tun lokacin da ya bada sanarwar cewa zai fitar da wannan waka a shafinsa na facebook.

Abubakar Damisa dan asalin jihar Kano mai shekaru 22 kuma kwararren masanin Computer, mawaki ne da ya maida hankali wajen wakokin Hip-hop da kuma soyayya, wanda hakan ya bashi damar jan zare cikin sahun matasan mawaka masu tasowa.

 

A hirar da jaridar Arewa Times tayi dashi a jiya ya bayyana mata cewa shifa babbar manufarsa shine ganin ya cigaba da kayatar da masoyansa, sannan ya yabawa masoyansa bisa irin gudummuwar da suke bashi ta goyon bayansu.

Domin Saurarar sabuwar wakar sai ka danna alamar sautin dake kasa:

Domin Yin Downloading sai ka danna “Download Now”

 

Arewa Times

12-10-2018

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *