Wasanni

Nijeriya ta lallasa Seychelles 3-0

Ahmed Musa ya shiga takarda inda ya zura kwallo daya a wasan neman shiga kofin afrika da tawagar super Eagles ta Nijeriya suka yi da kasar Seychelles wanda aka tashi 3-0.

Dan wasan ya fara zura kwallo a ragar abokan adawar Nijeriya  cikin minti sha biyar da fara a wasan da aka buga ranar asabar 8 ga watan Satumba.

Dan wasan baya  Chidozie Awaziem ya kara ma Nijeriya kafin a tashi zuwa hutun brabin lokaci na wasa wanda aka buga a filin wasa na kasar abokan adawar su.

Bayan minti sha biyu da dawowa hutun rabin lokaci dan wasa Odion Ighalo ya kara zura kwallo a ragar abokan adawar Nijeriya wanda bayan wannan ba’a kara wani ba.

Nijeriya tana da maki uku cikn wasa biyu da ta buga na wasannin neman shiga gasar kofin afrika. Wasan ta na farko na rukunin E Nijeriya ta sha kashi a hannun kasar Afrika ta Kudu inda aka tashi 2-0.

Wasan ta na uku na rukuni Nijeriya zata fafata da kasar Libya a gida ranar 10 ga watan Oktoba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *