Labarai

Jirgin kasar Abuja Ya Halaka Hanu 53

Jirgin kasa dake safara tsakanin garin Kaduna zuwa Abuja ta halaka shanu 53 sakamakon hatsarin da ya faru ranar lahadi 9 ga wata.

Kwamishnan yan sanda na jihar Kaduna Ahmad Abdulrahman ya sanar cewa lamarin ya faru ne a garin Kasarami dake karamar hukumar Kagarko na jihar.

A cewar makiyayin dake kiwon shanun ya fita da su ne bayan ya samu labarin karya cewa jirgin bata aiki ranar lahadi.

Ya kara da cewa lamarin ya faru yayin da makiyayi dake kiwon su ke hanyar sa zuwa jihar Katsina duk cikin aikin kiwo.

Kamar yadda ya bayyana jama’ar garin sun firgita domin suna zaton cewa yan ta’adda ne suka kawo farmaki.

Kwamishnan yace kwantar da hankulan jama’a tare da jaddada cewa babu wani ran dan Adam da aka rasa kana yace rundunar yan sanda zata cigaba da iya bakin kokarin ta wajen tabbatar da zaman  lafiya a yankin

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *