Wasanni

Har Yanzu Akwai Aiki A Gaban Mu –Kociyan Nijeriya

Kociyan ‘yan wasan Super Eagles ta Nijeriya Gernot Rohr ya bayyana cewa har yanzu akwai aikin a gaban sa duk da cewa sun samu nasara akan kasar Sychelles a ranarAsabar din data gabata. Tawagar kwallon kafa ta Super Eagles ta doke ta Seychelles da ci 3-0 a wasan neman shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka fafatawar rukuni na biyar a wani wasa mai wahala da aka buga a kasar ta Sychelles. Nijeriya wadda ta ziyarci Seychelles ta fara cin kwallo ta hannun Ahmed Musa minti 15 da fara buga wasa, sannan Chidozie Awaziem ya kara ta biyu tun kafin aje hutun rabin lokaci sannan bayan da aka dawo ne Odion Igahalo ya ci ta uku a bugun fenariti.

Daya wasan rukuni na biyar din tashi suka yi babu ci tsakanin Afirka ta Kudu da Libya a kasar ta Africa ta kudu wadda a wasan farko ta doke Nijeriya har gida daci 2-0. Da wannan sakamakon Libya tana mataki na daya a kan teburi da maki hudu, sai Afirka ta Kudu ita ma da maki hudu, sannan Nigeria ta uku da maki uku sai Seychelles wadda bata da maki a matsayin ta karshe.

Super Eagles za ta karbi bakuncin Seychelles a ranar 22 ga watan Maris din shekara ta 2019 sannan daga baya zata kai ziyara kasar Africa ta kudu kafin t agama wasa kuma da kasar Libya Za a buga gasar cin kofin nahiyar Afirka a shekarar 2019 a kasar Kamaru.

Leadership

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *