Labarai Siyasa

Ban Fita Daga PDP Ba -Shekarau

A Safiyar Yau an wayi gari da labarin cewa tsohon gwamnan Kano Malam Dr. Ibrahim Shekarau ya fice daga Jam’iyyar PDP sanadiyyar Rikicin da ya kunno kai bayan rushe shugabancin Jam’iyyar na jiha da uwar Jam’iyyar ta kasa tayi wanda hakan bai masa dadi ba.

Sai dai yanzu haka kai tsaye tashar Radio ta Aminchi wadda mallakin daya daga cikin jiga-jigan Jam’iyyar PDP na Kano ne kuma wanda ke da Kyaky-kyawar fahimta da malam Shekarau ta rawaito Malam Shekarau kai tsaye Inda ya musanta wannan labarin yace yana nan daram a Jam’iyyar sa ta PDP.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *