Labarai

‘Yan Sanda Sun Hana Hawan Dokin Kara A Kano

Rundunar Yansandan Jihar Kano ta haramta Hawan Dokin kara a fadin Jihar Kano har sai Baba ta gani.

CZ: 5700/KS/PRD/VOL.3/26 31st August, 2018
………………………….
………………………….
SANARWA
Rundunar Yansandan Jihar Kano ta haramta Hawan Dokin Kara da ake gudanarwa a wasu Unguwani cikin Birnin Jihar Kano da kewaye. Wannan hani ya zama wajibi duba da yadda Samari suke gangamin shirya irin wannan Hawan kuma daga karshe yake haifar da fadace-fadacen Daba da kuma tunzuri bayan muzgunawa al’umma babu gaira babu dalili. Haka zalika, an samu Shugabannin Al’umma daban-daban da suka yi korafin wannan Hawa da yake Uzzurawa Al’umarsu.
A sakamakon haka, Rundunar ta hana duk wani Hawan Dokin Kara da aka shirya a Jihar kano har sai Baba ta gani. Kuma an baiwa Baturan Yan Sandan Jihar Kano umarnin karsu kara karba ko amincewa wadanda suka rubuto takardar neman izinin gudanar da Hawan Dokin Kara. Da fatan Iyaye zasu gargadi Yayansu, sannan Samari su kaucewa dukkanin abinda ya saba tsarin doka da kuma abinda zai haifar da tashin hankali, Asarar Rayuka, da Dukiya ko kuma tashin tashi na.
Idan kunne ya ji, to jiki ya tsira, haka kuma idan an ki ji, to ba’a ki gani ba.

MAI SANARWA

SP. MAGAJI MUSA MAJIA,amnipr
KAKAKIN RUNDUNAR YANSANDA
A MADADIN KWAMISHINAN YANSANDA
JIHAR KANO

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *