Kimiya Labarai

An Gudanar Da Taron Abuja Social Media Master Class

ABUJA SOCIAL MEDIA MASTER CLASS

Taro ne da aka gabatar a farkon makon nan a birnin tarayya Abuja wanda ya samu halartar cibiyoyi, jamian kamfanunuwa na yanar gizo-gizo, Yan jaridu, masana a bangaren Computer da yanar gizo-gizo taron wanda wani matashin marubuci daga kudancin kasarnan Mr. Ukwu Sampson Ebube ya jagoranta an tattauna batutuwa da dama tsakanin mahalartan daga ciki akwai:

Yadda ake bunkasa cinikayya ta yanar gizo-gizo.
Banbancin farashin yanar gizo-gizo yadda zaka bi domin samunsu cikin sauki.
Yadda ake amfani da shafukan yanar gizo-gizo
Yadda Mutum zai tsaya da kafarsa a yanar gizo-gizo
Yadda zakayi saurin isar da sako a yanar gizo-gizo
Yadda ake tallata haja a yanar gizo-gizo
Yadda ake dakile yaduwar karerayi a yanar gizo-gizo, da tantance labarin kanzon kurege.
Yadda ake iya tantance ingancin mutum daga profile dinsa na facebook
Yadda ake tantance ingancin abokai, banbancin yawa da kuma ingancin mabiya a yanar gizo-gizo.
Yadda zaka kare kanka daga afkawa dana sani a Social Media.

Batutuwan da dama domin an gabatar da batutuwa sama da shafi dari da ashirin (120) a taron.

A yankin arewacin Nigeria cibiyar bincike da wayar da kan alumma akan yanar gizo-gizo ta Sharfadi.com ta samu amsa gayyatar wannan taro kuma mun samu halarta tare da yan uwa Nura Ibrahim Maigoro da Yusuf Idris Bugawa

Bayan karawa juna sani da akayi a taron, mun kuma samu alaka da masana daga bangarori daban-daban na kasar nan.
An kawo tunani iri-iri a wannan taron matasa sun baje basira matuka da gaske.
A yayin taron an yabawa cibiyar Sharfadi saboda abubuwa uku kamar yadda aka fada a wurin taron.

Wayar da kan dalibai yan arewacin kasarnan akan yadda zasu ci jarrabawar Jamb a shekarar da ta gabata da kuma sauran batutuwa na harkar ilimi. (anyi laakari da littifin Sharfadi mai suna Takardar Sanin Makama Ga Daliban Da Zasu Zana Jarrabawar Jamb)
Wayar da kan alumma akan sani da kuma amfani da Computer cikin harshen Hausa (laakari da littafin sharfadi mai suna Mu Koyi Computer A Saukake)
Wayar da kan alumma akan yadda ake amfani da yanar gizo-gizo, wanda shine daman babban abinda cibiyar ta sanya a gaba.

#BasheerSharfadi #ASMM #AbujaSocialMediaMasterClass #SocialMedia #Nigeria #Abuja #UkwuSampson #Facebook #Twitter #WhatsApp #Youtube

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *