Labarai Rahotonni

RIKICIN’YAN DABA A KANO Laifin waye? -Nasir Zango

RIKICIN’YAN DABA A KANO
Laifin waye?


Yau ma dai an fafata tsakanin’yan kwamitin da suka fafari kasuwar sayar da wiwi a hauren Ailan (Island kofar Nasarawa) da kuma wasu matasa masu makamai wadanda ake zargi baraden wani kusan gwamnatin Kano ne maisuna Hon.Murtala salisu Gwarmai.Yau dai tunda karfe 1 na rana aka batara har takai shi Hon.Gwarmai ya sami rauni a kokon kansa,bayan da ‘yan kwamitin suka yunkurin kama wasu kannensa da suka yi hijira daga unguwar bayan sara suka da ake zargin sun aikata tun bara.Daga bisani ne ana tsaka da sallar magariba kuma sai rikici ya zama sabo,har takai an raunata guda daga cikin kwamnadojin kwamitin mai suna Jamilu Aliyu.ziyarar da nakai sashin tsautsayi na asibitin Murtala na sami jamilu da Kwance cikin halin mutu ko kai rai kokai,Kwamdan’yan kwamitin dai yace Hon Gwarmai ya dade yana addabar su tare da shakikansa irinsu Nazifi da musaddiq da sauransu,wadanda yace sune shafaffu da mai da suka zame musu kadangarun bakin tulun dake kawo wa aikinsu na wanzar da zaman lafiya da hana shaye-shaye tazgaro.’Yan kwamitin sunce albarkacin mukamin gwamnati da Gwarmai ke dashi da kusancinsa da lamba daya yasa koyaushe yana musu gadara tare da hana kwamiti katabus wajen yin aiki akan kannensa.yan kwamitin sunce suna cikin sallar magariba ne dakarun Gwarmai suka afka musu har takai an illata kwamanda Jamilu Aliyu wanda suka ce dama,an taba yi masa barazanar kisa har sunje sun yi rapot gun’yansanda.Haka kuma sunce sau dadama Hon.Gwarmai yana yawan yi musu barazanar cewar shifa ko kisa yayi to na mai takanas ne,sai dai naso jin ta bakin shi Hon.Gwarmai amma ban samu damar hakan ba,kasancewar wayar sa a kashe take.Wani abu da yakamata a duba shine a shekarar bara irin wannan ta faru kuma yan kwamitin sunce sun kai kara amma har yanzu basu ga an dauki mataki akan Gwarmai ba.Zan cigaba da lalubar Gwarmai domin shima naji daga bakin sa.Amma kafin nan,shin mai girma gwamna yasan yadda yan kwamitin Nasarawa suka fatattaki masu dillacin kwayoyi da wiwi daga bakin Ailan? Shin ko Essalansi yasan cewar Gwarmai baya zaman lafiya da yan kwamitin unguwar tasu,ta haure Ailan? Shin ko mai girma Dr Abdullahi Umar Ganduje Khadimul islam yasan cewar akwai kannen Hon.Gwarmai da ake zargin suna kawo wa aikin kwamitin tazgaro? Kullum dai shugabannin mu kira suke a zauna lafiya,to me yasa Hon Gwarmai ya zama gagarabadau har takai yayi kaurin suna akan harkar banga? Kodai sharri ake masa domin a bata masa suna? Shin mai girma gwamna kasan kuwa waye Gwarmai a idon al’ummar unguwar sa ta kofar nasarawa? Shin me sauraro a ganin ka waye yake daure wa daba gindi ne a Kano? Allah ya taimaki Kano ya wanzar mana da zaman lafiya Allah ya tona asirin wanda duk ke da hannu wajen tayar da hankulan jama a,idan a boye yake Allah ka tona masa asiri idan kuma a bayyane yake sabo da yana da karfi Allah ka karya shi kowaye shi.
Nasir Zango.

1 COMMENTS

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *