Labarai

Uwar Gidan Gwamnan Borno Nana Kashim Shetima Ta Yi Raba Raguna Dari

A ranar Lahadin karshen wannan mako ne, uwar gidan gwamnan jihar Borno, Hajiya Nana Kashim Shettima, ta raba raguna 100 ga malamai da matan da suka rasa mazajen su ta dalilin rikicin Boko Haram, a Maiduguri, domin su gudanar da layya. An bayar da wannan tallafin ne a karkashin gidauniyar uwar gudan gwamnan; Gidauniyar Baiwa Zawarawa, Marayu tare da Malaman Tsangaya Tallafi (SOWT).

Hajiya Nana Shettima ta ce ta bayar da wannan taimakon ne ga wadannan yanki na al’umma ne domin gudanar da bikin babbar sallah (Layya) cikin nishadi da farin ciki, tare da yin kira zuwa gare su da cewa su ci gaba da addu’ar samun dawamamen zaman lafiya ga kasa baki daya. “mun bayar da wannan taimako ne domin mu karfafa su kuma da alfarmar babbar sallah mai zuwa, ta layya”.

Inji ta. Daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar wannan tallafin, Malama Yagana Mustapha, ta bayyana matukar godiyar su ga uwar gida; Hajiya Nana Kashim Shettima, bisa wannan kyauta wadda ta bayyana da cewa sun ji dadin ta sosai, kuma zasu gudanar da bikin babbar sallah cikin farin ciki.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *