Nishadi

Akshay Kumar Yafi Kowa Mabiya Na Instagram A Bollywood

Shahararren jarumin fina-finan Bollywood Akshay Kumar, ya zama na farko da ya fi sauran jaruman fina-finan Indiya samun masu bibiyarsa a shafin sada zumunta na Instagram.
A yanzu haka Akshay na da masu bibiyarsa da suka kai miliyan 20.
A ranar Litinin 20 ga watan Augusta, 2018, shafin Instagram ya ba wa Akshay lambar yabo saboda kai wa wannan mataki.
A shafinsa na Instagram, Akshay Kumar ya rubuta cewa, ‘ Wannan wata sabuwar dama ce da na samu daga mutane masu kima a Instagram. Ina mai farin cikin sanar da ku cewa na zamo jarumin Bollywood namiji na farko da na ke da masu bibiyata a Instagram miliyan 20.Nagode wa masu bibiyata kwarai da gaske.’
A cikin watan Augustan 2018, an saki fim din Akshay Kumar mai suna Gold da ya samu gagarumar karbuwa.
BBChausa.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *