Addinai Labarai

Hisbah Ta Kama Motocin Giya 20 A Kano

Hisbah Ta Kama Motocin Giya 20 A Kano

 

Daga watan Janairu na wannan shekarar izuwa yanzu hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama motocin giya guda 20 da ake shirin kutsawa dasu sassa daban-daban na jihar.

Mataimakin Shugaban hukumar Barrister Nabahani Usman ne ya bayyana hakan, tare da irin namijin kokarin da hukumar keyi wajen dakile fatauci da shan miyagun kwayoyi a jihar, da kuma sanya ido wajen magance badaloli iri-iri .

 

Wannan yana cikin manyan ayyukan da hukumar Hisbah ta sanya a gaba tun farkon kafa wannan hukuma.

 

Muna fatan Allah ya kara musu kwarin gwiwar cigaba da dakili irin wadannan batutuwa.

 

#ArewaTimes #Hisbah #Kano #KNSG

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *