Wasanni

Liverpool Ta Kai Karar Mo Salah Wajen ‘Yan Sanda

Kungiyar kwallon kafa ta Liberpool ta shigar da karar dan wasanta Mohamed Salah ga jami’an ‘yan sanda bayan wani hoton bidiyo ya nuna dan wasan karara yana latsa wayar salula alhalin yana cikin tukin mota.

Rundunar ‘yan sandan birnin Merseyside ta tabbatar da mika bidiyon ga wani sashenta don gudanar da binciken da ake tuhumar dan wasan dashi. An yi ta yada bidiyon a shafukan sada zumunta da ke nuna Salah wanda ya ci wa Liverpool kwallaye 44 a kakar da ta gabata, na latsa wayar a cikin motarsa wadda magoya bayansa da kananan yara suka kewaye ta.

Liverpool ta ce, za ta dauki nata matakin kan batun a cikin gida, amma ta ce, kawo yanzu, babu wani karin bayani da za a sake ji daga bakinta ko kuma daga bakin dan wasan na Masar. Koda yake babu cikakken bayani kan ranar da aka dauki hoton bidiyon amma hukumomi suna nan suna bincike kuma zasu bayyana irin laifin da dan wasan ya aikata da kuma irin hukuncin da za’a yi masa.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *