Wasanni

Facebook Zai Haska Wasannin Laliga Kyauta

Kamfanin Facebook ya sanar da matakin fara nuna wasannin gasar La Liga ta kasar Sipaniya kai-tsaye kuma kyauta a wasu kasashen kudancin Asiya. Za a fara kallon wasannin na kwallon kafa kai-tsaye a kafar Facebook a kyauta bayan kamfanin na sada zumunta ya sanar da kulla yarjejeniya da hukumar gasar La Liga ta Spain.

Wata sanarwa da kumar La Liga ta fitar ta ce Facebook zai nuna dukkanin wasannin gasar 380 na kakar bana da za a soma a ranar Juma’a. Masu amfani da Facebook da ke sha’awar kwallon kafa za su kalli wasannin a kasashen India da Afghanistan da Bangladesh da Nepal da Maldibes da Sri Lanka da kuma Pakistan.

Facebook zai ci gaba da nuna wasannin kai-tsaye daga wannan kakar har zuwa kakar wasanni biyu masu zuwa, a karkashin yarjejeniyar. Facebook ya ce zai fara nuna wasannin ne ba tare da saka wani talla ba sai dai kuma gasar ta La liga da kuma kamfanin na facebook ba su bayyana kudin da suka amince ba na yarjejeniyar.

Ana ganin wannan babban mataki ne ga Facebook na nuna wasannin gasar kwallon afa Kuma duk da cewa kasashen yankin sun fi sha’war kwallon kuriketi da kuma wasannin kwallon kafa na Firimiyar ingila amma kuma sha’war kwallon kafa na ci gaba da karuwa a yankin musamman a India.

Ana dai ganin nuna wasannin kyauta da Facebook zai yi zai kashe wa wasu kafofin da ke nuna wasanni, musamman kamfanin Sony da aka ruwaito ya biya dala militan 32 don ‘yancin nuna wasannin gasar La Ligar Spaniya a yankin tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018. Kuma fara nuna wasannin kwallon kafa a shafukan sada zmunta na intanet kai tsaye kuma kyauta, wasu na ganin babbar barazana ce ga masu ‘yancin nuna wasannin kwallon kafa a kafofin talabijin.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *