Labarai

ZABEN ZIMBABWE : Mnangagwa Ya Lashe Zabe.

Dan takarar jam’iyyar ZANU – PF kuma shugaban kasar zimbabwe Emmerson Mnangagwa ne ya lashe zaben kasar da aka gudanar A makon nan, Hakan ya biyo bayan sanarwar sakamakon zabe da hukumar zaben kasar dake burnin Harare ta Ayyana A safiyar yau juma’a..

Mnangagwa ya samu kaso 50.8% cikin dari na kuri’un da aka kada tsanin sa da abokin gwabzawarsa Nelson Chamisa na babbar jam’iyyar hamayya ta (MDC) wanda Ya samu kaso 44.8% cikin dari.

Mnangagwa wanda Tsohon shugaban kasar ta Zimbabwe ne wanda kuma ake wa lakabi da “KADA” saboda irin salon siyasar sa, ya kasance shugaba tun A watan Nuwanbar shekarar da ta gabata A wani mataki na kawo karshen gwamnatin Tsohon shekararren shugaban kasar Robert Mugabe.

Jim kadan da sanarda sakamakon zaben Sabon Shugaban ya mika sakon godiya zuwa ga Al’ummar kasar ta cikin shafin sa na twitter.

LABARI : SA’ID AMINU SA’ID

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *