Wasanni

Mece ce makomar Thiery Henry da Morata?

Mece ce makomar Thiery Henry da Morata?

 

Har yanzu Manchester United tana fatan sayen dan wasan Inter Milanmai shekara 29, Ivan Perisic kuma ta za ta sayar da dan Faransa, Anthony Martial, mai shekara 22, ne kawai idan za ta iya samun dan kasar Croatian din, in ji (Mirror).

Har yanzu dai sayen dan wasan bayan Tottenham dan kasar Belgium, Toby Alderweireld, mai shekara 29, na cikin abubuwan da Manchester United ta fi bai wa fifiko, amma kungiyar ta Landan tana son miliyan 55 ko kuma a saka Anthony Martial cikin yarjejeniyar, in ji (Independent).

Mai kungiyar Tottenham Spurs Daniel Levy ya ce ya yi imanin cewa zai iya sayen dan wasan tsakiyar Aston Villa dan Ingila, Jack Grealish, mai shekara 22, kan kudi fan miliyan 20, in ji (Mirror).

Liverpool ba ta da burin sayen dan wasan bayan BesiktasDomagoj Vida, mai shekara 29, duk da cewa an alakanta ta da dan wasan na Croatia, in ji (Liverpool Echo).

Chelsea ta ce AC Milan ta biya fan miliyan 62 idan tana son ta sayi dan wasan gaban Spain, mai shekara 25, Alvaro Morata, in ji (Sky Sports).

Jami’ai daga Chelsea sun tafi Italiya domin sayen dan wasan bayan Juventus,Daniele Rugani, mai shekara 23, amma ba sa son su biya fan miliyan 40 kan dan wasan na Italiyan, in ji Times.

Mai kungiyar Chelsea Roman Abramovich da kuma daraktar kungiyar Marina Granovskaia za su gana a birnin Nice domin su tattauna game da abin da suke son cimma a kasuwar musayar ‘yan wasa, in ji (Standard).

Sai dai kuma, yadda Chelsea ta sayi tsohon golan Ingila mai shekara 38, Robert Green, ya bai wa masu taimaka wa kocin kulob din, Maurizio Sarri, mamaki – domin sunan dan wasan ba ya cikin sunayen ‘yan wasan da bangaren da ke nemo ‘yan wasa ya bayar ba, in ji jaridar Times.

Barcelona ta shirya domin karbar tayin fan miliyan 27 da Everton ta yi wa dan wasan bayan Colombia, Yerry Mina, mai shekara 23, in ji (Goal).

Dan wasan tsakiyar Everton Davy Klaassen, mai shekara 25, yana tattaunawa da Werder Bremen kan tafiyar fan miliyan 13, in ji (Liverpool Echo).

 

Dan wasan bayan Manchester United dan kasar Ingila Luke Shaw, mai shekara 23, ya ce “zai mini sauki in bar” kulob din amma yana son ya samu sabuwar yarjejeniya.

Yarjejeniyarsa ta yanzu za ta kare ne a lokacin bazara mai zuwa, in ji (Guardian).

Crystal Palace da Everton suna son sayen dan wasan tsakiyar Roma mai shekara 27 Maxime Gonalons kan kudi fan miliyan 10, in ji (Standard).

Tsohon dan wasan Arsenal da Faransa Thierry Henry yana nazari kan damarmaki aikin koci hudu bayan kungiyar gasar Championship, Aston Villa, ta yanke shawarar ci gaba da aiki da Steve Bruce, in ji (Mirror).

Fenerbahce na son daukar aron dan wasan bayan Stoke Bruno Martins Indi, mai shekara 26, na tsawon kaka daya, in ji (Takvim – ta Turkiya).

 

Rahoton Sashen Hausa Na BBC.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *