Addinai Labarai

Darikar Qadiriyya Ta Bude Masallaci Da Kuma Maukibin Nasiriyya A Kano

An gudanar. Da maukibin NASIRIYA Tare da bude masallaci a gidan kadiriyya.

A safiyar yaune aka gudanar da bikin maulidin shekh Nasiru KABARA. Wato Nasiriyya bayan kammala zagayenne daga gidan kadiriya zuwa gwale aka gudanar da taron bude masallacin Wanda dan majalisar jiha mai wakiltar municipal HON. Baffa Babba dan agundi ya Gina a gidan kadiriya.
Taron Wanda ya sami halartar. Mai martaba sarkin kano MAL. Muhd. Sunusi ||tare mai girma gwamnan kano Dr. Abdullahi umar ganduje. Da shugaban karamar hukumar birni Hon. Sabo Muhd Dantata. Da mataimakin shugaban majalisar dokokin kano. Kabiru Alasan rurum. Da sauran manyan baki daga sassa daban daban.
Dayake jawabi agurin taro gwamnan kano Dr. Abdullahi umar ganduje ya sha alwashin Gina makarantarnan ta turasu tare da bayyana irin gudun mawa da halifan kebayarwa.
Dayake jawabi shugaban darikar. Shekh karibullahi shehk Nasiru KABARA . ya yabawa gwamnatin kano da irin gudun mawar da yake bayarwa Abangare adini tare da yabawa Wanda ya Gina masallaci wato HON. Baffa Babba da agundi .sannan kuma ya Nada baffan a matsayin mukkadamin kadiriya.
Akarshe dai mai martaba sarkin kano MAL. Muhd. Sunusi II. Ya kaddamar da masallacin tare da Jan sallar Azzahar a masallacin……

Rahoto: Shafi’u Bako

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *