Labarai Siyasa

Shin Koda Gaskene? Ganduje Na Shirin Dawo Da Shekarau Da Kuma Takai APC

Shin Koda Gaskene? Ganduje Na Shirin Dawo Da Shekarau Da Kuma Takai APC

Rahotanni da ke yawo a da’irar siyasar jihar Kano na nuna cewa, tsohon Gwamnan jihar Malam Ibrahim Shekarau da kuma dan takarar Gwamnan jihar Malam Salisu Sagir Takai na fecewa daga Jam’iyyar PDP zuwa APC.
Wasu makusantan Shekarau sun tabbatar da cewa, Gwamna Ganduje ya gana da su domin su dawo APC. Wanda dama Shekarau a ciki ya ke shigar Kwankwaso ne ya sa shi fecewa.
Hasashe na cewa Shekarau zai samu damar yin takarar Sanatan Kano ta tsakiya, kujerar da Kwankwaso ke kai a yanzu. Kana kuma Takai ya zama mataimakin Ganduje, wanda dama mataimakin sa a yanzu Farfesa Hafizu Abubakar ya bayyana cewa, yana tare da Kwankwaso.
Wannan turka-turka ta biyo bayan ganawar sirri da Ganduje ya yi da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, jim kadan bayan ficewar Kwankwaso. Kuma an jiyo Shekarau na kwatanta Kwankwaso a matsayin mara adalci a harkokin siyasar sa ta baya.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *