Wasanni

Ko Kasan ‘Yan Takarar Gwarzon Dan Kwallo Na Duniya?

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi na cikin
sahun ‘yan wasa 10 da Fifa za ta zabi gwarzon
dan wasan duniya na bana.
Antoine Griezmann da Kylian Mbappe da kuma
Raphael Varane da suka lashe wa Faransa kofin
duniya suna cikin wadanda ke neman lashe
kyautar.
Akwai kuma Luka Modric dan wasan Real Madrid
da ya jagoranci Croatia zuwa wasan karshe a
gasar cin kofin duniya a Rasha.
Sai dai Neymar na Brazil ba ya cikin jerin ‘yan
wasan guda 10 da Fifa za ta zabi gwarzo a bana.
Messi da Ronaldo ne suka mamaye kyautar a
tsawon shekaru 10, amma ana ganin a bana ana
iya samun sauyi.
Wasu na ganin yadda Messi da Ronaldo suka
kasa taka rawar gani a gasar cin kofin duniya a
kasashensu, na iya bude kofa ga Antoine
Griezmann da Kylian Mbappe da kuma Luka
Modric.
Antoine Griezmann shi ne wanda ya lashe kofin
duniya ya kuma taimaka wa Atletico Madrid lashe
Europa League.
Modric ma na da damar lashe kyautar a bana
saboda rawar da ya taka a gasar cin kofin duniya
da kuma taimakawa Real Madrid lashe kofin
Zakarun Turai sau uku a jere.
Modric ne ya karbi kyautar gwarzon dan wasa a
gasar cin kofin duniya.
Zai kasance karon farko da za a samu wani dan
wasa da ya ratso tsakanin Ronaldo da Messi ya
lashe babbar kyautar a kwallon kafa.
Sai dai kuma Ronaldo wanda ya karbi kyautar sau
biyu a jere, na iya lashe kyautar a karo na uku a
jere bayan ya taimakawa Real Madrid kare kofin
Zakarun Turai karo uku a jere.
Duk da cewa Messi ya lashe La Liga da Copa de
Ray kuma wanda ya fi yawan zura kwallo a raga a
Turai a kakar da ta gabata, amma rashin taka
rawar gani a gasar cin kofin duniya zai iya hana
wa kaftin din na Argentina da Barcelona lashe
kyautar a karo na shida.
‘Yan wasa 10 da ke takarar gwarzon duniya
Cristiano Ronaldo (Portugal) – Real Madrid
Kevin De Bruyne (Belgium) – Manchester City
Antoine Griezmann (Faransa) – Atletico Madrid
Eden Hazard (Belgium) – Chelsea
Harry Kane (Ingila) – Tottenham Hotspur
Kylian Mbappe (Faransa) – Paris Saint-
Germain
Lionel Messi (Argentina) – Barcelona
Luka Modric (Croatia) – Real Madrid
Mohamed Salah (Masar) – Liverpool
Raphael Varane (Faransa) – Real Madrid
Fifa za ta tace ‘yan wasan zuwa uku a watan
Satumba wadanda za a zabi gwarzo daga cikinsu.
Tuni aka fara jefa kuri’a a shafin FIFA.com, har
zuwa 10 ga Agustan 2018 da za a rufe kada
kuri’a.
Tsarin jefa kuri’a
Masoya kwallon kafa na cikin wadanda ke taka
rawa wajen zaben gwarzon duniya da gwarzon
koci a bangaren maza da mata.
Haka kuma tsarin zaben gwarzon dan wasan na
duniya ya kunshi masu ruwa da tsaki a harkar
kwallon kafa da suka hada da kaftin da masu
horar da ‘yan wasa da kuma ‘yan jarida.
An rarraba yadda bangarorin za su kada kuri’a.
Kaftin na tawagogin kasashen duniya suna da
kashi 25 na kuri’a.
Masu horar da ‘yan wasa suna da kashi 25.
Masoya kwallon kafa da suka kada kuri’a a shafin
fifa suna da kashi 25.
Sai kuma rukunin ‘yan jarida 200 da aka ware wa
kashi 25.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *