Audio Labarai Rahotonni

Audio: Yadda Wani Mutum Ya Yiwa Abokin Aikinsa Yankan Rago A Kano. Laraba 20-07-2018

HIRAR JARIDAR AREWA KAN KISAN KAI DA AKA SAMU A KANO.

JARIDAR AREWATIMES: Assalamu Alaikum.

MAL. JAFAR: wa’alaikumu Salam

JARIDAR AREWATIMES: muna so muji sunan ka.

MAL. JAFAR: sunana Jafar nasidi mai tasa.

JARIDAR AREWATIMES: menene alakar ka da mamacin.

MAL. JAFAR: kanin Matata ne.

JARIDAR AREWATIMES:inah son muji menene ya faru da shi.

MAL. JAFAR: suna zaune da matarshi wajen karfe 8:30pm, sea aka kira shi a waya, sea ya ajiye wayar shi tare da sanar da matarsa akwai wanda ya kira shi, abokin aikinsa, sea ya canja kaya yasa jallabiya ya tafi wajen da aka kira shi.

Dama wanda ya kirashi abokin sana’ar sane (suna aikin kafitancin a layin Aminu kano).

Bayan ya tafi, wajen karfe 9-10pm sea ta kiran wayar shi bata same shi bah, tun a daren ta sanar da wanda yakamata ta sanar (kan ta nemishi bata sameshi) aka sanar da Yan Sanda.

Har zuwa safe ba’a same shi bah, sea daga baya aka ce an gano gawarsa a tambari an yankashi. Yan sanda suka daukeahi suka kai shi asibiti, akai gwaje-gwajen da zaai masa aka dawo da gawar gida akai masa sallah.

Wannan shine a takaice abinda ya faru. Amma shi abokin nasa, matarsa ta sheda mana cewa “ya dawo gida kamar karfe sha biyun dare zuwa sha daya da rabi, hankalinsa a tashe, ya canja kaya, ya kashe wayoyinsa sannan ya bata ta ajiyemasa, kuma ya sanar da ita cewa yay tafiya (zuwa lagos, da sake tambayar sa yace abuja). Kuma ba’a ganshi har yanzu bah.

JARIDAR AREWATIMES: kuma dama shi bai saba shigowa gida a wannan lokacin bah. (wato shi abokin nasa).

MAL. JAFAR: a’a shima ya fita amma ya dawo kamar yadda na fada maka a baya, amma shi ya dawo gida a wani yanayin da bai taba shigowa bah.

JARIDAR AREWATIMES: yanzu ba’a samu nasarar kama shi bah.

MAL. JAFAR: aa yanzu dea komai yana hanun yan sanda. Kuma sun karbi wayoyinsa da kuma details din abinda ya faru.

Domin Sauraron Cikakkiyar Tattaunawar Sai Ka Danna Sautin Dake Kasa

Domin yin downloading sai ka danna “Download Now”

 

Rahoto: Umar Abdullahi & Salim Sani Shehu

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *