Shirye-Shirye

Hasken Yara 002 -Salim Sani Shehu

Masu bibiyar mu a wannan shafin, barkan mu da wannan lokaci, barkan mu da sake haduwa a cikin wani shirin na hasken yara kashi na biyu.

Idan mai bibiyar bai manta bah, mun tsaya a lokacin da muka kawo ma’anoni tare da duba ga yadda rayuwar yaro take a matsayin yarinta, da kuma lokutan (shekarun da yake a matsayin yaro).

Yau zamuyi duba ne ga muhalli, idan aka ambaci muhalli ana nufi wani guri da abu mai rai (mai hankali ko marar hankali) ke samu dan gabatar da al’amuran sa na sirrin koh hutu wanda ba kowa yake su ya sani bah.

Tarbiya tare da al’ada na samu wane daga muhalliln da mutum ya fito, shi yasa a wata karin magana ta hausawa ke cewa (kowanne tsuntsu kukan gidan su yake) abin nufi muhallil shine mataki na farko da yaro ke sanin kansa da kuma sanin halin da yake na rayuwa.

A bangaren ilimi yaro na samu ilimi a matakin farko ne a muhallin da ya taso, haka zalika tarbiya, tsafta, koh kuma nutsuwar rayuwa. Shi yasa yakan kasancewa daga lokacin da yaro ya taso a muhalliln da akwai nutsuwa da kwanciya hankali koh wadatar zuci, zaka ga yana samun yabo tare da fatan dorewa a haka bisa ga ambaton “kai amma yaron nan dan kirki ne”, idan kwa ya kasance sabanin haka haka zalika zaka ga yana samun yabo wanda bai kamata bah.

A duba na muhalli na samun kyakyawar tarbiyya, kuma koh ilimi koh abinda muka ambata a sama, zamu ga cewa al’ummar da yaro ya taso na zama daya daga cikin wanda take sauya rayuwa ga yaron.
Akwai karin maganar hausawa da suke cewa (Amma Albasa batai halin Ruwa ba)
I dan aka samu akasin yadda tarbiyan gidan su take, haka ne zai kara tabbatarwa cewa abokanai kokuma al’ummar da yaron ya taso na bada gudunmawa wajen ganin ingantuwar ta koh kuma akasin haka.

Zamu tsaya anan sea kuma Allah ya kaimu a cikin shirin na gaba.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *