Labarai

Ayyuka Hudu (4) Da Hukumar INEC Keyi Dangane Da Katin Zabe A Halin Yanzu -Arewa Times

Cigaban Tattaunawa Da Garba Lawan Muhammad Jami’in Yada Labarai Na Hukumar Zabe Ta Kasa Reshen Jihar Kano.

 

Arewa Times: Wannan Batun Rijista Da Akeyi Na Katin Zabe, Ga Wadanda Nasu Ya Bata Ko Kuma Suke Da Wasu Gyare-Gayare Da Suke So A Yi Musu Akan Sa?

 

Garba Lawan Muhammad: To Yanzu Akwai Aiki Da Mukeyi Da Ake Kiransa Cigaba Da Rijistar Masu Kada Kuri’a, A Wannan Aikin Ayyuka Guda Hudu (4) Mukeyi A Lokaci Daya.

  1. Aiki Na Farko Ana Yiwa Wadanda Basu Yi rijista Da Ba Ana Musu Rijista Kila A Wancan Lokacin Basu Cika Shekara Sha Takwas (18) Ba, Ko Kuma Wani Dalili Ya Hanasu To Yanzu Ana Musu Rijista.
  2. Na Biyu Ana Yiwa Duk Wanda Misali Ya Canja Wurin Zama Kila Da Kayi Rigista A Kano Yanzu Kana Lagos, In Kana Wata Karamar Hukuma Ma Kila Bebeji Yanzu Ka Koma Kunci To Shima Za Kaje Hukumar Zabe Ta Canja Maka Wurin Jefa Kuri’a Kuma Ta Canja Maka Kati.
  3. Abu Na Uku Da Mu Keyi Shine Wanda Katinsa Ya Bata Ko Ya lalace Shima Zai Zo Hukumar Zabe Yace Nayi Rijista A Waje Kaza Amman Yanzu Katina Ya Bata Ko Kuma Ga Katin Amman Kunga Ya Lalace Ko Ya Kode, Abinda Za Muyi Shine Kawai Zamu Duba Rijistarmune Muga Cewa Akwaika Din ga Hotonka Din Ga Komai Shikenan Za’a Cike Maka Wani Form Za’a Baka Wani Katin.
  4. Aiki Na Hudu (4) Da Mu Keyi Shine Da Kayi Katin Kuma Katin Naka Yana Nan Kuma Lafiyarsa Kalau Amman An Samu Wani Kuskure, A Wajen Sunanka Ko Ranar Haihuwa Ko Wani Abu Dai Mai Kama Da Haka, To Shima Akwai Form Din Da Za’a Cike Maka Sai Ayi Maka Wannan Gyaran Sai A Baka Wannan Katin Da Wannan Sabon Gyaran Da Za’ayi, Wannan Shine Ayyuka Guda Hudu Da Mu Keyi A Yanzu.

 

Arewa Times: Misali Kamar Wadanda A Wancan Lokacin Shekarunsu Basu Kaiba Sai Yanzu Shin Akwai Wani Abu Da Ake Bukatar Suje Dashi Na Daga Takarda Ko Wani Abu Wurin Yin Rijistar?

 

Garba Lawal Muhammad: A’a Gaskiyar Magana Shine Za Kaje Ne Kawai, Amman Idan ba’a Yarda Da Shekarunka Ba Za’a Ce Ka Kawo Takardar Shaidar Haihuwa Domin A Tabbatar Cewa Eh Kaine, Amman Indai Ba Haka Ba Kazo Kace Shekarana Sha Takwas (18) Kuma Aka Ga Eh Ka Kai Sha Takwas Din (18) Babu Wani Abu Za’a Yi Maka Rijista.

 

Arewa Times: Kuma Hakan Ba’a Ganin Zai Bada Dama Ga Wadanda Ba ‘Yan Kasa Ba Suyi Amfani Da Wannan Damar Suma Su Mallaki Katin Zabe?

 

Garba Lawal Muhammad: Kamar Yadda Ka Sani Shine Cewar Doka Tace Sai ‘Yan Nigeria Ne Za Suyi Rijista, Duk Wanda Yayi Kokarin Yin Hakan Kuma Aka Kama Shi Zai Fuskanci Hukunci Mai Tsanani Kamar Yadda Doka Ta Tanada, Amman Dai Daga Abinda Muke Gani Shine Cewar A Yanzu Dai Bamu Samu Wani Rahoto Na Cewar Wasu ‘Yan Wata Kasa Suna Rijista A Yayin Wannan Aiki Ba.

 

Domin Saurarar Wannan Tattaunawa Sai Ka Danna Sautin Dake Kasa:

 

 

Domin Sauke Tattaunawar Akan Wayarka Sai Ka Danna “Download Now” .

 

Akwai Cigaban Tattaunawar Gobe Idan Allah Ya Kaimu.

 

Rahoto: Basheer Sharfadi & Sa’id Aminu Sa’id.

11-07-2018.

 

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *