Shirye-Shirye

Shirin Hasken Yara 001 – Salim Sani Shehu

HASKEN YARA 01

Yaro shine wanda yake a tsakanin shekarun 0-15 kuma makamantam haka, yaro ana alakantashi da sabon halitta a farkon matakin shekarun sa na haihuwa, da kuma lokacin da ya fara tasowa.

Yaro na samun madubin rayuwarsa a inda ya taso, ma’ana dea yaro na samun halayar inda ya taso bisa ga tasiruwanta a jikinshi.

Wani yaron yana tasowa a cikin, bakin talauci inda yake kaiwa cewa, ya saba da yunwa, rashin tufafi koh kuma muhalli mai kyau.

Wani yaron na tasowa a cikin matsakacin rayuwa na samun abin ci, muhalli da sutura daide gwargwado.

Wani kuma yaron yana tasowa a matsayin samu ishashe da kuma samun abin da ya ke bukata.

Yana yin da yaro ya taso ke sanya shi samun nishadi gabanin rayuwarsa.

Misali wanda ya taso a matakin kunci koh rashin sa: kan gina rayuwarsa kan tunani da hasashen cewa “in na girma na samu kaza koh kaza, zanyi kaza koh kaza”, wani sa’in kuma in yana rayuwa cikin abokanansa masu shi sai kaji yana hasashen cewa “zanse gida irin su wane ko kuma mota koh sutura iri kaza”. Sakamakon cewa ya taso ne a kan bautan da yake ciki ko kuma yake fama da shi.

Toh haka misalin ma yake ga wanda ya rayu a cikin halin da yake ciki.

Na tambayi abokin aiki Sa’id Aminu Sa’id Na Aminchi Radio shin wanene yaro
“hausawa nacewa yaro sabon mutum, kuruciya kuma dangin hauka, Idan aka ce yaro ana nufin mutum mai karancin shekaru, wanda bashi da ilimin yau da kullum, kuma mai bukatar da ta rataya a kan iyeyenshi, na tufatarwa, da kuma shayarwa.”

Sea dea matsayin ma’anar ta yaro na bambamta tsakanin wani zuwa wani.

Haka ma Nura Haruna mai Karfe ma ya bayyana yaro a matsayin
“Yaro ko yarinta – Yarinta itace a lokacin da yaro yake cikin wasu kananan Shekaru run daga tsakanin shekaru 1 zuwa 9 . a wannan tsakanin ake koya ma yaro dabi’a da tarbiyya bar zuwa lokacin da zai kai girman da zai mallaki hankalin kanshi . ma’ana zuwa shekaru 18 daga nan ya shiga sahun da baza’a kirashi da yaro ba”

Haka yake ga duk wanda ka ambata ga wannan batu na yaro abin dubawa kawai dea shine yaro wani mutum ne mai tallafuwa ga mutum:
“Yaro: Mutum Karami wanda bai mallaki hankalin kansa ba, ma’ana yana da kuruciya” shine abin da Basheer Sharfadi ya ambata game da yaro.

Wanna. Dea shine mafari ga batun domin samu mafita game da yaro da kuma yarintarsa.

Ku cigaba da kasancewa da mu awannan shirin na HASKEN YARA.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *