Labarai

Shin Ko ‘Yan Najeriya Da Basa Kasar Zasu Mallaki Katin Zabe? Amsa Daga Hukumar INEC

A Jiya Litinin 09-07-2018 Jaridar Arewa Times Ta Tattauna Da Garba Lawan Muhammad Jami’in Yada Labarai Na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta Ta Kasa Reshen Jihar Kano Dangane Da Batun Rijistar Masu Kada Kuri’a Da Hukumar Ke Gudanarwa.

 

Ga Kadan Daga Cikin Tattaunawar:

Arewa Times: Za Muso Muji Dangane Da Dalibai Ko ‘Yan Nigeria Dake Zaune A Kasashen Waje Shin Meye Matsayinsu Dangane Da Rijistar Zabe Da Akeyi?

 

Garba Lawan Muhammad: To Jama’a Assalamu Alaikum, Kamar Yadda Ka Sani Cewar Duk Wanda Zai Jefa Kuri’a Saidai Yayi Rijista A Nigeria, Ba’a Jefa Kuri’a Kan Nigeria A Kasar Waje, Saboda Haka Duk Wanda Yake So Ya Jefa Kur’a Sai Ya Dawo Nigeria Yazo Yayi Rijista Inda Yake So Zai Jefa kuri’a, Wannan Shine Abinda Ake Ciki A Yanzu.

 

Domin Sauraron Wannan Bayanin Cikin Sauti Daga Bakin Mal. Garba Lawan Muhammad Sai Ka Danna Sautin DaKe Kasa.

Cigaban Tattaunawar Zaizo Muku A Gobe Laraba Cikin Yardar Allah, Domin Jin Irin Aikin Da Hukumar INEC Din Takeyi A Yanzu.

 

Rahoto: Basheer Sharfadi & Sa’id Aminu Sa’id

10-07-2018.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *