DANDALIN NISHADI

DANDALIN NISHADI : Ina Kallon Talabijin Baituka Suka Zo Mun – Inji Matashin Mawaki – AK BOY.

SA’ID AMINU SA’ID @ 08146858250 TES KAWAI.

Hausawa na cewa rana bata karya sai dai uwar diya taji kunya , to ranar batayi karyar ba kuma uwar diyar bata ji kunyar ba.

Mai Karatu Barka da war haka kamar yadda muka alkawarta muku cewar daga wannan rana ta LITININ 09/07/2018 Zamu fara kawo muku shira da fittatun mawaka da masana harkokin nishadi ta cikin wannan shafi mai suna DANDALIN NISHADI.

Filin DANDALIN NISHADI na wannan makon ya samu sukunin ganawa da matashin Mawaki ABDURRAHMAN KAMAL wato AK-BOY Wanda ya shafe shekaru biyu cur yana gudanarda harkar waka.

Ga yadda Tattauwar mu ta kasance.

AREWA TIMES : Jama’a zasu so su san waye AK-BOY ?

AK-BOY : To Assalamu Alaikum, Kamar yadda aka sani suna na ABDURRAHMAN KAMAL Wanda aka fi sani

da AK-BOY, kuma An haife ni A jihar katsina A shekarar 2000 , Nayi karatu A wata

makaranta dake unguwar badawa A garin kano. Kuma yanzu haka ina A matsayin Aji biyar din

sakandire wato SS.2

AREWA TIMES : Ya akayi ka shiga Harkar waka ?

AK-BOY : Eh Na fara harkar waka ne dalilin ina sha’awar nishadi musamman wakokin HIP-HOP, na dade

ina son naga nima na fara rera waka da kaina, inda nayi ta kokarin yin hakan sai daga karshe

wata rana “INA KALLON TALABIJIN NAJI BAITUKA SUNA ZUWAR MUN” Haka ne yasa na yanke

shawarar tafiya wurin rera waka (STUDIO) A kano da taimakon wani mawaki Bello Sanayya.

AREWA TIMES : Kamar ana ganin matasan mawaka irinka suna yin koyi ne da Marigayi LIL AMIR, Ya abun

yake A wajen ka ?

AK-BOY : A gaskiya dai ni bana koyi da marigayi LIL AMIR amma ina son wakokin sa musamman

( I Am The Boss ).

AREWA TIMES : Ya zuwa yanzu wakoki nawa ka rera ?

AK-BOY : Wakoki na Biyar.

AREWA TIMES : A cikin wakokin ka wacce kafi so ? ina nufin BAKANDAMIYA.

AK-BOY : Waka ta ta uku Wato “SUN SARA ” Ita gaskiya abinda take nuni dashi shine kafin na rera waka ta

ta farko a (STUDIO ) An yi ta yi mun dariya da cewar wai bazan iya ba, har naje nayi ta A haka,

bayan  na dawo gida sai jama’a suka yi ta ganin kokari na suna yaba mun sosai har Ana bani

kyauta ,  shi yasa nayi ta nace “SUN SARA”.

AREWA TIMES / AK-BOY (DARIYA !!!) “SUN SARA ”

AREWA TIMES : A ina kake samun kudin buga waka kasancewar ka matashi ?

AK-BOY : Mamana ce take biya mun da kudinta.

AREWA TIMES : AK-BOY Menene sakon ka ga Al’umma ?

AK-BOY : Sako na  A guji raina mutum , saboda ba’a san irin baiwar da ALLAH yayi masa ba.

AREWA TIMES : To mun gode kuma muma mun “SARA”

AK-BOY : (DARIYA !!) Nima na gode.

ku biyo mako mai zuwa domin ganin mu da wani bakon, kafin sannan nake cewa “KUMA KU SARA”

 

SA’ID AMINU SA’ID @ 08146858250 TES KAWAI

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *