Labarai Uncategorized

MAIDUGURI : Ana Korar Yan’ Gudun Hijira Zuwa Gidajen Su Na Asali

Tun A ranar Sha bakwi ga watan juli ne dai Rundunar sojin Najeriya Ta sanar da cewa sama da yan gudun hijira mutum dubu biyu ne suka koma gidajen su bayan gudun tserewa mayakan kungiyar boko haram da suka yi, inda suka koma garin Guzamala dake jihar borno A Arewa maso gabashin kasar ta Nigeria, waccan sanarwa dai ta fito daga Hafsan Rundunar Sojin kasar wato Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai wadda ya fitar tun A wancan Lokaci.

Hakan dai ya biyo bayan wani rahoto na musamman da wani sashin Rundunar na Operation Lafiya Dole ya fitar na cewar sun kawo karshen mayakan kungiyar ta boko haram.

Tun daga wancan lokaci ne dai yan gudun hijira da dama suka rika komawa gidajen nasu ciki kuwa harda wasu karin mutane dubu daya da dari biyu wadanda suma suka koma muhallan su dake Garin Bama duk dai A jihar Ta Borno.

To sai dai wani Abun takaici shi yadda ake ta samun karin hare-hare a wuraren da yan gudun hijirar ke komawa, Misali ko da A washe garin ranar aka fitar da waccan sanarwa sai da wani Bom ya fashe A garin Damboa Ana tsaka da shagulgulan bikin karamar sallah.

Kungiyoyin bada Agajin gaggawa dai na cigaba da Shawartar Rundunar da ta dakatar da yan’ gudun hijirar da komawa huhallen nasu na Asali.

LABARI – SA’ID AMINU SA’ID

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *