Labarai

Takaitattun Labarai

www.arewatimes.com.ng

Labarai:

-A yaune Matasa masu yiwa kasa hidima kimanin 25, 000 da doriya aka sa ran yaye su. Tsarin Da qka fara shi tun a shekarun 1975 karkashen jagorancin shugaban mulkin soji na wancan lokacin.

-Wata babbar kotu a Najeriya ta amince ta saurari karar da wasu lauyoyi suka shigar na bai wa majalisar dokokin kasar umarnin tsige Shugaba Muhammadu Buhari.

-Wani bangare daga cikin jam’iyya mai mulki ta APC wadanda an yi imanin cewa suna samun goyon baya daga wasu jiga-jigan gwamnatin da ke kokarin dakile yunkurin shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin ta-zarce a shekara ta 2019, sun ayyana kafa wata sabuwar jam’iyya.

-Dan takaran Shugaban Kasa a karkashin inuwar Jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido ya ce jam’iyarsa ta PDP ce kadai ke da maganin matsalolin da suka dabaibaye Najeriya, domin APC ba za ta iya.

-Jami’an rundunar ‘yan sanda na tawagar yaki a fashi da makami , ta kama wadanda ake zargi da kashe wani babban jizo na jam’iyyar APC ta jihar Imo, Amos Akano.

-Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC za ta yanke hukunci kafin tsakiyar watan Juli kan ko za ta bar kamfanin MTN ko ta dakatar da kamfanin ya ci gaba da amfani da zangon megahaz mai karfin 800 da ta mallaka da lasisin kamfanin Visafone .

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *