Labarai Wasanni

Tambuwal ya ba dan wasan Super Eagles kyautar gida

Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tabuwal ya bai wa dan wasan Najeriya Shehu Abdullahi kyautar gida da fili da kujerar hajji da kuma kyautar kudi a matsayin tallafi ga gidauniyarsa, kamar yadda dan wasan ya bayyana.

Dan wasan, wanda yake cikin tawagar da ta wakilci kasar a gasar cin kofin duniya a Rasha, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Litinin.

 

Mai taimakawa gwamman jihar kan yada labarai Abubakar Shekara ya tabbatarwa wa BBC labarin, kuma ya ce an ba shi filin ne don ya kafa wata Gidauniyar Wasanni wadda za a sanya wa sunan dan wasan.

Shehu Abdullahi wanda dan asalin jihar Sakkwato ne ya yaba wa gwamnan.

 

Kasar Argentina ce ta cire Najeriya daga gasar cin kofin duniya a matakin rukuni, bayan ta doke ta da ci 2-1.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *