Labarai Uncategorized

Na Kashe Mutum Tara Cikin Shekara Biyu -Inji Tsohon Dan Kungiyar Asiri

Na Kashe Mutum Tara Cikin Shekara Biyu -Inji Tsohon Dan Kungiyar Asiri

Daga Basheer Journalist Sharfadi

A jiya Laraba rundunar ‘yan sanda ta jihar Ogun ta cafke wani gawurtaccen dan kungiyar asiri da ya addabi jihar a Abeokuta.

Mutunin mai suna Gbenga Ogunsanya dan shekaru 22 yace mutum tara ya hallaka cikin shekaru biyu da ya shiga kungiyar asiri tsakanin 30 ga watan Mayu na shekara ta 2017 zuwa watan Maris na wannan shekarar ta 2018.

Ogunsanya wanda aka fi sani da Spartacus yana daya daga cikin mutane 48 da kwamishinan ‘Yan sanda jihar Ogun Ahmed Ilyas ya ayyana cewa sun addabi jihar.

Jaridar Independent ta rawaito wamishinan ‘Yan sandan na bayyana Ogunsanya a matsayin mafi hadari cikin ‘Yan kungiyar asirin dake jihar musamman ganin yadda ya zamo jagoran kungiyar asiri mafi hadari cikin kankanin lokaci kuma cikin karancin shekaru.

#ArewaTimes #NigerianPolice

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *