Rahotonni

AN KAMASHI BAYAN YAYI SATA A ASIBITI KOFA TAKI BUDEWA

Dubunsa Ta Cika Bayan Yaje Sata A Babban Asibitin Jahar Kaduna Bayan Kofa Taki Buduwa

        Daga Auwal M Kura

12/05/2018

Dubun Wani Baro Ta Dayake Shiga Dakunan Masu Jinya Dake Baban Asibitin Jahar Kaduna Na Yusif Dan Tsoho Da akafi Sani Da Asibitin Dutse Yana Dauke Dauke Ta Cika,

Andai Kamashine Bayan Yayi Shigar Burtu Ya Shiga Bangaren Maza, Inda Yayi Kamar Yana Jinyar Wanine,inda Bayan Kowa Yayi Barci Yabi Ya Kwashe Musu Wayoyi,

Sai Dai Bayan Kwashe Wayoyin Ne Asirinsa Ya Tono Bayan Ya Tarar Da Kofar Sashin A Kulle Kamar Yadda Aka Saba Idan Dare Yayi Ana Kulle Duk Kofofin Shashi Na Asibitin,

Yazu Haka Dai Duk Wadan Da Ya Satarwa Wayoyin Sun Karbi Kayansu Sannan Suka Damkawa Jami’an Tsaron Dake Kula Da Asibitin Barawo Domin Cigaba Da Bincikar Sa

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *