Labarai

JAMI’AN TSARO SUNYIWA MAJALISAR NAJERIYA KAWANYA

DA DUMI DUMI:
JAMI’AN TSARO NA MUSAMMAN SUN MAMAYE MAJALISA

     Daga Auwal M Kura

02/05/2018

Yanzu Haka Wasu Jami’an Tsaro Na Mussaman Cikin Shirin Kota Kwana Sun Mamaye Lungu Da Sako Na Majilisar Najeriya,

Jami’an Da Suka Bayyana Ayau 2/5/2018 Ciki Da Wajen Majalisar Fuskokinsu Duk Arufe, Ba’asan Dalilin Bayyanarsu A Majalisar Ba .
Sai Masu Fashin Baki Kan Siyasa A Najeriya Wasu Na Ganin Wannan Wani Matakine Na Kara Tsaurara Tsaro A Majalisar Duba Ga Dambarwar Data Faru Wanda Wasu Yan Daba Suka Shiga Suka Sace Sandar Iko Ta Majalisar Dattijai, Sai Dai Wasu Kuma Na Ganin Ana Tsorata Majalisar Da kuma Alakanta Hakan Bisa Wani Rahoto Da Majalisar Zata Karba Yau Na Bantun Tsige Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ,

Sai Dai Majalisar Ta Ummarci IG Na Kasa , Ibrahim Idris Da Kuma Darekta Na Hukumar , DSS, Lawal Daura Su Canja Salon Shigar Jami’an Domin Kaucewa Abunda Ka iyya Zuwa Ya Dawo.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *