Anayi Muna Jin Dadi

DALILIN DA YASA ZANYI TAKARA A 2019 — KWAMRED ABBA AUWAL TAHIR (DAN IYYA)

Dalilin Da Yasa Zanyi Takara — Inji Comrd Abba Auwal Tahir
(Dan Iyyan T/Wada)

Daga Auwal M Kura

Matashin Dan Gwagwarmayan Nan Dake Jahar Kaduna , Comrade Abba Auwal Tahir Ya Bayyana Dalilansa Na Tsayawa Takarar Dan Majalisar Tarayyar Najeriya Mai Wakiltar Karamar Hukumar Kaduna Ta Kudu.

Yayin Tattauna Da Wakilmu Kwamared Abba Tahir Auwal, Ya Bayyana Cewa Zai Fito Takara Ne Mussaman Duba Ga Yadda Kasar Ke Bukatar Matasa,Masu Sabbin Tsare Tsare Da Kudurori, A Wannan Lokaci,
Inda Ya Kara Da Cewa”Zamuyi Takara Ne Domin Ingata Rayuwar Al-ummar mu Mussanman Matasa ,Da Ababen More Rayuwa,Ta Hanyar Karfafasu Basu Nema Musu Aiyukanyi Da Ilimi,Kiwon Lafiya Don Ganin Sunyi Rayuwa Cikin Aminci ”

A Karshe Kwamred Abba Auwal Tahir, Yayi Kira Ga Matasa Dasu Shigo Harkar Siyasa Domin Neman Mukamai Don Kawo Cigaba Mai Ma’ana A Wannan Kasa Ta Najeriya, Ba Tare Da Nuna Tsoro Ko Fargaba Ba Domin Kuw Yanzu Lokaci ne Na Matasa Da Matasa.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *