Labarai

RUNDUNAR SOJIN NAJERIYA TA KAMA YAN TA’ADDA 38

RUNDUNAR SOJIN NAJERIYA TAYIN NASARAR KAMA MUTUM 38 MATSAFA DA MASU FASA BUTUTUN MAN FETUR

D

AGA AUWAL M KURA
22/04/2018

Rundunar Sojin Najeriya A ranar Asabar 21/04/2018 Tace Tayi Nasarar Kama Wasu Mutum 23 Da Uku Da Take Zargi Da Aikata Fashi,tsaface tsaface Da Garkuwa Da Mutane,

Haka Zalika Rundunar Tayi Nasarar Kama Wasu Mutum 15 Bisa Fasa Bututun Man Fetur Kana Rundunar Ta Gano Jarkoki Guda 31Wanda Suke Zuba Man Fetur din.

Shugaban Rundanar Soji Ta 81 Maj-Gen. Enobong Udoh, Ya Bayyana Ga Manema Labarai A Bataliya Ta 174 Dake Ikorodu A jahar Lagos.
Udoh, Wanda Ya Wakilci Shugaban Sojin Na Yankin Brig.-Gen. Moundhey Ali, Yace Sun Kama Yan Ta’addan Ne A Gurare Da Ban Daban , Bayan Wani Rahoto Da Suka Samu Ta Hanyar Fikira Da Sirri.

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *