Rahotonni

Yaushe Boko Haram Zasu Kare a Sambisa ?

Rundunar Sojin Najeriya ta kubutar da fararen hula 149 daga hannun ‘yan ta’addar Boko Haram a dajin Sambisa da suke fake wa a cikinsa.
Rundunar sojin ta sanar da cewa, ta kai farmaki kan kungiya a dajin Sambisa.
Mataimakin Kakakin Rundunar Sojin Kanal Onyeama Nwachukwu ya sanar da cewa, mutanen sun hada da mata 54 da yara kanana 95.
Nwachukwu ya kara da cewa, ana kula da lafiyar mutanen da aka kubutar daga hannun kungiyar kuma a yayin farmakin an kashe ‘yan ta’adda da dama. Sai dai abunda wasu yan najeriya me tambaya shine shin yaushe Mayakan boko haram zasu kare a dajin na sambisa . wanda shine babbar tungar mayakan sama da shekaru 7 .

#Trt #ArewaTimes

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *