Kimiya

YADDA ZAKA KOYI SIDDABARU A KAFAR YADA LABARAI

ANA YI MUNA JIN DADI 002
YADDA AKE KWAFAR RUBUTU
Jama’a Assaamu Alaikum acikin shirin mu na yau zamuyi bayani akan yadda ake kwafar rubutu da kuma yadda ake kai shi wani gurin misali daga facebook zuwa whatsapp ko wasu gurare makamantan su (copy & past) sai a biyo mu.

1. Idan kana amfani da browser kamar su opera fire fox uc browser yadda zaka yi kwafi shine zaka danne dan yatsan ka a farko ko karshen rubutun da kake son kwafa zai baka “select” ko “copy” sai ka shiga zaka ga ya fara highlighting ya sa kala sai ka janyo shi har zuwa inda kake so sai ka danna copy zai saka maka “copied” shike nan.
2. Idan kana amfani da application na facebook kuma to idan zaka yi copy kawai ka danne kan posting din zai yi maka copy ko ya baka alamar copy sai ka danna, sai dai shi baya baka damar ka kwafi iya inda kake so sai dai gaba ki dayan posting din in yaso sai kaje ka ciri iya inda kake so.
3. A WhatsApp kuma yadda ake yin copy shine idan ka danne ka rubutun da kake son yin copy zaka ga yasa kala akan sa, sannan a sama ya baka wasu alamu kamar zakayi forwarding to acikin alamun zaka ga wani shape kirar “square” sai ka danna zai saka maka “messege copied” shikenan, sai dai shi baya baka damar ka kwafi iya inda kake so sai dai gaba ki dayan posting din in yaso sai kaje ka ciri iya inda kake so.

BAYAN NA KWAFI RUBUTU YAYA ZAN SANYA SHI A WANI WURIN KO NA TURAWA WANI??
Abinda zaka yi shine kawai kaje ko ma wane guri ne indai wurin rubutu ne misali wps ko inbox din ka ko wall din ka da kake posting ko group ko page din ka sai ka danne dan ya tsanka zai baka “past” sai ka danna shikenan rubutun zai kawo a wajen sai ka tura ko kayi posting din sa.

Zamu dakata anan sai a shiri na gaba.

Daga

Basheer Journalist Sharfadi

1 COMMENTS

LEAVE A RESPONSE

Your email address will not be published. Required fields are marked *